Janar Yahaya kan hare-haren cibiyoyin soji: Kwamandoji zan kama da laifin sake kai hari

*Rundunar Sojin Saman ta yi amai ta lashe kan harin Jihar Yobe
*Lallai za a gudanar da bincike – Gwamna Buni

Daga MAHDI M. MUHAMMAD a Abuja

Babban Hafsan Sojojin Ƙasa na Nijeriya, Laftanar Janar Faruk Yahaya, a jiya Laraba a Abuja ya sha alwashin cewa, daga yanzu zai kama kwamandoji a dukkan matakai da alhakin kai hare-hare kan cibiyoyin soji da suka haɗa da sansanonin soji, barikai da sauransu.

Babban Hafsan Sojojin, wanda ya faɗi haka a yayin rufe taron Manyan Hafsoshin Sojojin da aka yi a Abuja, ya kuma bayyana cewa, halin sanyin jiki da wasu kwamandoji ke nunawa, ba za a lamunta ba.

Ya kuma umarci kwamandojin da su tabbatar da cewa sojoji su na ci gaba da kasancewa cikin shiri da taka-tsantsan a kodayaushe, don guje wa duk wani hari na bazata daga maƙiya ƙasa.

“Ina so na tunatar da Kwamandojin Rukuni kan buƙatar tabbatar da isasshen tsaro na sansanoninsu, barikinsu, da sauransu. Za a ɗauki kwamandojin da alhakin duk wani matsalar tsaro. Muhimmancin shugabanci ba za a iya wuce gona da iri ba musamman a aikin soja,” inji shi.

Ya ce, “alhakin shugaba ne ya raya ya kuma sami amincewar muƙarrabansa. Amincewa da aka gina akan kyawawan halaye shine ginshiqi don ingantaccen jagoranci wanda aka tsara don samun sakamako. Don haka, Kwamandoji a kowane mataki dole ne su samar da nagarta da kyakkyawan shugabanci yayin da suke bin manyan ƙimar Sojojin Nijeriya.”

“Dole ne kuma kwamandojin su tabbatar da cewa sun ci gaba da kasancewa masu kula, ginawa da samun mutunci da amincewa da na kusa da su don yin jagoranci yadda ya kamata. Na ba da umarni cewa a samar da kayayyaki na horon jagoranci kuma a yi amfani da su a duk cibiyoyin horon mu don haɓaka aiki da ayyukan duk jami’anmu,” inji shi.

Shugaban ya ƙara da cewa, “a yayin gudanar da ayyukanmu, dole ne Kwamandojin su tabbatar da cewa sojojin su na ci gaba da kasancewa cikin kula da taka tsantsan a kowane lokaci don gujewa duk wani hari na bazata daga abokin gaba. Haka nan aikin Kwamandoji ne su kula da albarkatu da dabaru da aka sanya musu don gudanar da ayyuka don samun sakamako.

Ba za a amince da halayen sanyin jiki daga kwamandoji ba. Kamar yadda koyaushe nake faɗi, rashin nasara shi ne gazawa ba tare da la’akari da yanayin ba. Don haka, na ba da umarni ga sassan da suka dace da su fito da hanyoyin da za a bi don tantance ayyukan kwamandoji yayin gudanar da aikinsu.”

“Bugu da ƙari, kwamandoji dole ne su ci gaba da ba da haɗin kai da aiki tare tare da ayyukan sauran hukumomin tsaro da masu ruwa da tsaki yayin da suke havaka sabbin dabaru, don mamaye maƙiyi ta amfani da dabaru iri ɗaya. Dole ne kwamandoji su kasance masu ƙwazo wajen gudanar da ayyukansu. Dole ne ku shigar da yaqin cikin wuraren da aka sani da sanannun wuraren ‘yan ta’adda da masu laifi don kawar da su.”

Da ya ke roƙon ‘yan Nijeriya da su ba su goyan baya, Janar Yahaya ya ba da tabbacin cewa, a cikin kwanaki masu zuwa, za a ga ƙarin alamun inganta tsaro a duk faɗin ƙasar, ya ƙara da cewa, sojoji za su yi magana da ‘yan ta’adda, ‘yan fashi, masu garkuwa da mutane da sauran masu tayar da hankali da yaren da suke fahimta.

A cewarsa, “Ni kuma, ina neman fahimta da goyon bayan dukan ‘yan Nijeriya don ba mu damar yi wa kasa hidima kamar yadda ake tsammani. Ina tabbatar wa ‘yan Nijeriya cewa, a cikin kwanaki masu zuwa, za a ga karin alamun inganta tsaro a duk faɗin ƙasar. Ina so in yi amfani da wannan damar in shawarci waɗanda ke rura wutar rikicin da ake gani a duk faɗin ƙasar da su guji ayyukan rashin kishin ƙasa yayin da muke jajircewa don tabbatar da dawowar zaman lafiya a kowane yanki na ƙasar cikin lokaci mai nisa.

“Sojojin Nijeriya, cikin shirin doka, za su yi magana da ‘yan ta’adda, ‘yan fashi, masu garkuwa da mutane da sauran masu tayar da hankali a cikin yaren da suke fahimta yayin tabbatar da cewa duk ‘yan ƙasar da ke son zaman lafiya na wannan ƙasar za su ci gaba da harkokin kasuwancinsu na yau da kullum, da kuma gudanar da rayuwarsu ba tare da tsoro ko fargaba ba,” inji shi.

A wani ci gaban kuma, Shugaban Hafsan Sojojin Sama (CAS), Air Marshal Oladayo Amao ya faɗa wa sojojin sashen sojojin saman Nijeriya (NAF) na ‘Operation Hadarin Daji’ cewa wannan ba lokacin da za a yi sakaci ba ne ko a ɗauka cewa an shawo kan abokan gaba.

Ya qara da faɗa wa sojojin cewa, lokuta irin wannan suna kira da a ba su horo na musamman, faɗakarwa, da kuma mai da hankali kan aikin da ke gabansu.

Air Marshal Amao ya faɗi haka ne yayin da yake rangaɗin aiki na ‘Air Component’ ƙarƙashin tawagar ‘Operation Hadarin Daji’ (OPHD) a jihar Zamfara, inda ya kuma umarci sojojin da su ci gaba da mai da hankali tare da yin taka tsantsan yayin da suke yin haɗin gwiwa don kawar da ɗaukacin Arewa maso Yamma daga ‘yan bindiga da sauran masu aikata miyagun laifuka.

Ya ƙara da cewa, “hare-haren da ake kai wa ‘yan fashi da ayyukansu sun ci gaba da haifar da sakamakon da ake tsammanin saboda haka akwai buƙatar a ci gaba da mai da hankali da sa ido har sai yanayin tsaro ya inganta.”

Air Marshal Amao ya kuma jinjina musu saboda jajircewarsu, sadaukar da kai ga aiki da ƙudurin tabbatar da ganin an kawo ƙarshen yaƙi da ‘yan bindiga a Arewa maso Yamma.

Tun da farko, Kwamandan rundunar haɗin gwiwa na OPHD wanda kuma ya ninka matsayin Babban Jami’in Kwamandan Runduna ta 8 na Sojojin Nijeriya, Manjo Janar UU Bassey, ya yi wa CAS ƙarin haske kan ayyukan da ke gudana a jihar Zamfara da ma yankin Arewa maso Yamma gaba ɗaya.
Ya sanar da CAS cewa ayyukan sun ci gaba da ba da sakamako mai muhimmanci tare da lalata wuraren ɓarna da lalata su.

Manjo Bassey ya kuma gode wa CAS don tabbatar da cewa an ba da horo sosai da kayan aikin soji zuwa yankunan aiki a yankin.

Daraktan Hulɗa da Jama’a na rundunar sojojin saman Nijeriya, Air Commodore Edward Gabkwet a cikin wata sanarwa ta bayyana cewa, Shugaban ya kuma ziyarci sojojin sama da suka ji rauni a Cibiyar Kiwon Lafiya ta Tarayya da 207 ‘Quick Response Group’, Gusau inda ya ba su tabbacin jajircewar NAF wajen kula da lafiyarsu da samun cikakkiyar lafiya.

“Yana da muhimmanci a lura cewa Sojojin na NAF na musamman da na sama sun ci gaba da kasancewa manyan masu taimakawa da yanke shawara a yaƙin da ake yi da masu garkuwa da mutane a Arewa maso Yamma. Tabbas, a cikin watanni 2 da suka gabata, an kashe ‘yan ta’adda da yawa ta hanyar haɗin gwiwar ƙoƙarin da aka yi tsakanin ɓangaren iska, Sojoji na musamman na NAF da sauran ɓangarorin tsaro a wuraren yaƙi,” inji Kakakin NAF.

Wani labarin kuma, Rundunar sojin saman Nijeriya ta musanta rahotannin da ke alaqanta ɗaya daga cikin jiragen yaƙin ta da jefa boma-bomai da aka yi wa wata al’umma a jihar Yobe.

A cikin wata sanarwa a ranar Laraba, kakakin NAF, Air Commodore Edward Gabkwet ya bayyana cewa, hukumar ta gudanar da aikin ta a jihar Yobe a farkon watan.

“NAF ta gudanar da aikin ta na ƙarshe a jihar Yobe, ba ƙaramar hukumar Yunusari ba, a ranar 5 ga Satumba 2021 kuma abin tashin hankali ne,” inji shi.

Amma wasu majiyoyi da yawa sun tabbatar da cewa Jirgin yaƙin ya yi ruwan boma-bomai a ƙauyen kuma an samu asarar rayuka.

Kalaman kakakin NAF ya zo ne sa’o’i bayan da mazauna yankin Buwari da ke ƙaramar hukumar Yunusari suka ce an kashe mutane da dama yayin da wasu suka jikkata a harin bam ɗin da aka ruwaito.

Wannan yanki yana arewacin Yobe, kusa da yankin da ISWAP ke aiki, don haka yana iya yiwuwa jiragen sun yi niyyar jefa wa ‘yan ta’addana ne. Mazauna ƙauyen sun ce ba su da tabbacin ko jiragen na Nijeriya ne ko Nijar amma da wuya a ce ta Nijar ce tana cikin yankin Nijeriya.

Amma daga baya, NAF ta tabbatar da yin hakan ga mutanen Yobe, inda suka yi nadamar musantawa da farko. NAF ta tabbatar da cewa jirgin nata na yaƙi ya yi harbi cikin fararen hula yayin da yake kai farmaki kan ‘yan ta’addan ƙungiyar ISWAP a yankin Kanama, Yobe.

NAF ta ce, suna cikin nadama mara misatuwa na musanta lamarin da farko. A cewar Kakakin NAF, Edward Gabkwet, Kwamitin binciken da zai binciki lamarin.

A nata ɓangaren kuma, Gwamnatin Jihar Yobe ta tabbatar da cewa, za a kafa kwamitin bincike, domin gano gaskiyar abin da ya faru a yayin wannan aika-aikar.

Gwamnan Jihar, Alhaji Mai Mala Buni, shi ne ya bayyana hakan a jiya Laraba, ya na mai cewa, za a yi binciken ne, domin a tabbatar da masu hannu a cikin wannan lamari da hukunta duk waxanda aka samu da laifi ko sakaci.