Masu garkuwa sun kashe shugaban ƙungiyar Miyetti Allah kan miliyan N20 a Kaduna

Masu garkuwa da mutane sun kashe shugaban ƙungiyar Fulani ta Miyyeti Allah Cattle Breeder (MACBAN), na reshen ƙaramar hukumar Lere a Jihar Kaduna, Abubakar Abdullahi Dambardi, saboda gazawa da ya yi wajen biyan fansar milyan N20 da aka buƙata ya biya kafin a sake shi.

Sanarwar manema labarai da ta sami sa hannun shugaban ƙungiyar na jihar Kaduna, Haruna Usman Tugga, ta nuna ɓarayin sun halaka Dambardi ne da sanyin safiyar Juma’a a Lere.

Tugga ya bayyana cewa, masu garkuwar sun buƙaci a biya su kuɗi har Naira miliyan 20 amma N250,000 ne marigayin ya iya samarwa ta hanyar rance, lamarin da bai gamsar da ɓarayin ba wanda a ƙarshe suka kashe shi.

Ya ci gaba da cewa, ɓarayin sun ɗauki marigayin zuwa Saminaka sannan Mari zuwa babbar hanyar Zango inda a can suka halaka shi.

Daga nan, Tugga ya yi kira ga gwamnati da jami’an tsaro da su binciki lamarin tare da kamo waɗanda suka aikata wannan aika-aikar ba tare da ɓata lokaci ba.

Ya bayyana marigayi Dambardi a matsayin jakadan zaman lafiya a tsakanin al’ummar ƙaramar hukumar Lere da kewaye.

A cewar Tugga, “Haƙiƙa mun yi rashin
jagora nagari wanda jama’a ke martabawa, wanda ya kasance mai yi wa ƙungiya hidima da bunƙasa ta da kuma samar da daidaito a tsakanin mambobinta.”

MACBAN reshen Kaduna ta jajanta tare da miƙa ta’aziyyarta ga ‘yan’uwa da abokan marigarin bisa wannan rashi, tare da yin addu’ar Allah (S.W.T) Ya sanya Aljanna ta zama makomar marigayin, kana Ya bai wa ahalinsa haƙuri da juriyar rashin.

A hannu guda, Kwamishinan Tsaro da Harkokin Cikin Gida na Jihar Kaduna, Samuel Aruwan, ya tabbatar da aukuwar lamarin tare da cewa, gwamnan jihar, Nasir El-Rufai, ya nuna alhininsa kan faruwar hakan.