Daga UMAR GARBA a Katsina
Yan ta’adda sun sace sama da mutane 15 a yankin Ƙanqara da ke jihar Katsina tare da neman kuɗin fansa na Naira miliyan 150 kafin su sake su.
Mazauna garin sun shaida wa PREMIUM TIMES cewa ‘yan ta’adada sun kai hari garin ne a ranar Asabar da Lahadi tare da sace mata da ƙananan yara.
Duk da cewa ‘yan ta’addan da ke Arewa maso yamma sun kashe ɗaruruwan mutane, sai dai karɓar kuɗin fansa shi ne babban abin da suka sa a gaba.
“Da farko ‘yan bindigar sun sace mutane biyu ne a garin kafin harin da suka kai na ranar Asabar da Lahadi. Akwai mutanenmu da yawa a hannunsu,” in ji wani mazaunin garin wanda yake koyarwa a makarantar sakandaren garin Ƙanƙara a yayin da yake zantawa da majiyar Blueprint Manhaja ta wayar tarho. Ya kuma nemi da a sakaya sunansa saboda dalilai na tsaro.
Majiyar ta mu ta ce, bayan an sace mutanen, ‘yan ta’adda sun kira iyalansu ɗaya bayan ɗaya tare da shaida musu cewa za su saki ‘ya’yan nasu ne idan sun biya Naira miliyan 150.
Wata majiyarmu, Usman, ya ce, ya kwashe iyayensa daga ƙauyen zuwa Ƙanƙara.
“Ba zan iya ƙirga adadin sau nawa ‘yan ta’adda suke kawo hari wannan garin ba. Wannan kuɗin da suke nema, wa yake da irin wannan kudin? Da na ga mutane sun fara barin garin, ni ma sai na kwashe iyayena na tafi da su Ƙanƙara domin mu zauna a gidan da nake haya,” In ji shi.
Ya ce mutane da dama a garin sun gudu saboda tsoron sake kawo musu wani harin.
A yayin da aka tambaye shi game da biyan kuɗin fansa, malamin wanda yana cikin shugabannin garin, ya ce, “Muna tattaunawa da dukkan masu ruwa da tsaki a garin domin ɗaukar mataki na gaba.”
Wannan satar mutanen da aka yi ya faru ne kwanaki bayan da mataimakin sufeton ‘yan sanda na shiyya ta 14 da ke zaune a garin Katsina, Bello Shehu, ya bai wa kwamishinonin ‘yan sanda a Katsina da Kaduna umarnin farmakar ‘yan bindiga.
“Mataimakin babban sufeton ‘yan sanda ya bai wa kwamishinonin ‘yan sanda umarni da ke yankin da su tura dakaru na musamman domin su gudanar da atisaye na musamman da tarwatsa gungun ‘yan ta’addan da ci gaba da sa ido a dukkan yankunan da abin ya shafa a waɗannan jihohi.”
Dukkan rundunoni na musamman an sanar da su tare da ba su umarnin ci gaba da sintiri a yankin da ƙananan hukumomi da manyan hanyoyi da wuraren ibada da sauran wuraren taruka. An tura jami’ai masu sa ido domin tabbatar da ɗa’a da tabbatar da ayyuka da bin ba’asi a tsakanin jami’an,” in ji Umar Mohammed, mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan shiyya ta 14 kamar yadda ya bayyana a cikin jawabi.
