
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Babbar Kotun Tarayya a Kaduna ta bayar da belin tsohon Gwamnan jihar, Nasir El-Rufai na wani shari’a mai alaƙa da rashawa da Hukumar Yaƙi da Rashawa (ICPC) ta shigar akansa, inda kotun ta umarci ya cigaba da zama a hannun Hukumar har zuwa lokacin da zai kammala cika sharuɗɗan belin.
Mai Shari’a Rilwanu Aikawa ya yi hukuncin a yau Talata bayan ɗage batun daga ranar 1 zuwa 14 ga watan Afrilu, 2026, domin yin nazari akan buƙatun ɓangaren masu gurfanarwa da naasu bayar da kariya.
Alƙalin ya bayyana cewa, an bayar da belin ne akan Naira miliyan 200 da kuma mutane biyu da za su tsaya masa.
Kotun ta kuma umarci cewa wajibi ne ga waɗanda za su tsaya masa su miƙa fasfo ɗinsu na ƙasa-da-ƙasa, sannan dole da ne ɗaya daga cikin ya zama jam’i ne na gwamnati mai matsayi na 15 zuwa sama yayin da ɗayan kuma wajibi ne ya zama sanannen basarake.
Bugu da ƙari, kotun ta haramta wa El-Rufa’i furta wasu kalamai a bainar jama’a game da shari’ar kuma dole ne ya halarci dukkan zama da kotu ta kira.
Da yake ganawa da manema labarai, wani mataimaki ga tsohon gwamnan mai suna Lawal Hayatudeen Maƙarfi ya bayyana cewa kotun ta zayyano sharuɗɗa guda 10 da ake buƙatar El-Rufa’i ya cika kafin a sake shi.
Don haka ne zai cigaba da zama a hannun ICPC har sai ya kammala cika sharuɗɗan kafin ya bar komar hukumar a hukumance.
A wani ɓangare kuwa, Babbar Kotun Kaduna ta ɗage sauraron ƙorafin bayar da belin tsohon gwamnan akan wata shari’ar da ICPC ta shigar akansa zuwa ranar 21 ga watan Afrilu, 2026, lamarin da ke ƙara tsawaita shari’ar tasa.
