
Daga MUHAMMAD BALA GARBA
- Gobe ranar Independent,
Wahala ba mu daina sha ba. - Shekaru sittin da ɗori,
Ba mu sauya ginin ƙasar ba. - Ga shi ƴanci aka ba mu,
Bautuwa ba mu daina yi ba. - Ilimi an kassara shi,
Rashawa ba a bar batun ba. - Ba ruwan sha babu NEPA,
Me ya sa ba zan koka ba? - Babu noma babu kiwo,
Ba mu san daɗin ƴanci ba. - Lafiya an wargaza ta,
Shi ya sa ba zan murna ba.- Ga shi fetur na ta tashi,
Ga shi ba noma muke ba. - Ga abinci yana ta tsada,
Ba a ƴan salari muke ba.
- Ga shi fetur na ta tashi,
- Ga matasa babu aiki,
Kuma gwamnati ba ta kula ba. - Ba tsaro birni da ƙauye,
Ba mu san sanadin hakan ba. - Sai a saci uwa da ƴarta,
Har da Sarki ba a bari ba. - Matsaloli sun yawaita,
A ƙasarmu gidan su Baba. - Ajalinmu yana matsowa,
Ga ƙasar ba ta ɗau saiti ba. - Babu ƙarfi babu ƙarfe,
Ga shi ƴaƴa ba su tasa ba. - Ciki zafi waje ƙuna,
Ban ga amfanin ƴanci ba. - To ina zance na murna?
Tun da ba ƙoshi muke ba. - Me ya sa ma zan yi murna?
Ga hawaye bai tsaya ba. - To ina hujja na murna?
Ɗalibai ba a bar sata ba. - Me akai har zan yi murna?
Tallafi ba a mai da shi ba. - Shin ta yaya zan yi murna?
Ba a daina kisan kawai ba. - Babu amfani na murna,
A ƙasar da ake ta zamba. - Masu murna kuy abin ku,
Ɗan-Bala ba zai hakan ba. - Rabbana kai mana sauyi,
Don Rasulu ba Ka ƙi yi ba. - Rabbi ceci ƙasarmu Allah,
Don ba za Ka ƙi yin hakan ba. - Zan tsaya haka zana huta,
Ba ƙiyayya ni nake ba. - Na rufe da dubun salati,
Gun Habibu riƙon Suwaiba. - Alihi nasa har Sahabu,
Ambatonsu ba zan ƙi yi ba. - Ɗan-Bala ya rubuta waƙar,
Can a Borno ba zan ɓoye ba. - Baituka linta na tsara,
Don ba zan yi shuru a kai ba.
©️
Mohammed Bala Garba.
5:29pm
1 Oktoba, 2022.
Sabuntawa
12:31pm
30 Satumba, 2024.
