
Ofishin babban jami’in Majalisar Ɗinkin Duniya na musamman a yankin Sahel, ta fara bugu biyu na “Muryoyin Sahel: Tattaunawa, Hanyoyi, da Magani” a kan yunƙurin da aka samar da bikin ƙaddamar da shi a shekarar 2021.
Wannan shiri tare da haɗin-gwiwar Hukumar Shirin Ci-Gaba na MƊD (UNDP), da Ofishin MƊD Mai Kula da Yammacin Afirka da Sahel (UNOWAS), da kuma UNICEF, na da nufin ƙarfafa wa matasa gwiwa a matsayin muhimman abubuwan ci-gaba a yankin.
Yayin da yankin Sahel ke fuskantar manyan ƙalubale kamar sauyin yanayi, rashin tsaro, da kuma taɓarɓarewar tattalin arziƙi, an tsara shawarwari na bana ne domin ƙara ƙaimi ga matasa, musamman mata, da kuma magance takamaiman buƙatunsu da damuwarsu.
Shirin na neman inganta tallafin da Majalisar Ɗinkin Duniya ke bayarwa don ci-gaban zamantakewa da tattalin arziƙi mai ɗorewa a duk faɗin Sahel.
Tattaunawar, wacce Daraktocin yankunan Majalisar Ɗinkin Duniya ke jagoranta, za ta binciki jigogi huɗu masu muhimmanci a cikin makonni huɗu, wato daga 30 ga Satumba zuwa 25 ga Oktoba, 2024.
Jigogin sun haɗa da; yin amfani da fasahar dijital don ci-gaba, haɓaka ilimi ga mata, bincika hanyoyin kasuwanci don ƙalubalen zamantakewa da tattalin arziƙi, da haɓaka shigar mata cikin siyasa.
Muryar Sahel ba wai ta na bada ƙafa ga ƴan Sahel don yin hulɗa kai-tsaye tare da jagorancin Majalisar Ɗinkin Duniya bane kawai, yana zama wata muhimmiyar dama ga Majalisar Ɗinkin Duniya don daidaita dabarunta na samar da zaman lafiya, kwanciyar hankali, da wadata a yankin Sahel.
Ta hanyar ba da fifikon shiga tsakanin matasa da ƙarfafawa mata, shirin na da nufin samar da sabbin shugabannin da suka shirya don tunkarar matsalolin yankin.
Nasarar wannan shirin za ta kasance abu mai muhimmanci wajen samar da makoma mai ɗorewa ga yankin, da tabbatar da cewa an ji kuma an aiwatar da ƙungiyoyin matasanta.
