Yanzu ta ina za mu bi mu tafi Kaduna?

Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA

Gaskiya hari kan jirgin ƙasa da ya tashi daga babban birnin Nijeriya Abuja da ke arewa ta tsakiya zuwa Kaduna da ke Arewa maso yamma abin tashin hankali ne da ban tsoro. Tsoron ya fi tada hankali ne don an ɗauka jirgin na ƙasa ne mafi zama mai tsaro don akwai jami’an tsaro da ke yi ma sa rakiya da kare lafiyar fasinjoji a cikin kowane taragu. Jirgin ya haɗa da taragun masu hannu da shuni da kuma na matsakaita ko talakawa.

Duk da haka ai jirgi ɗaya ne kuma direba ɗaya ne ke tuqa shi kazalika burin dai shi ne a isa Rigasa a Kaduna. Indai bambancin wajen cajin waya ne da kujeru masu laushi ko daraja, hakan bai sa an saka jami’an tsaro a wannan taragu an bar wancan ba. Jirgin yak an tashi ko daga tashar Idu ko Kubwa a Abuja ya riqa tafiya sulululu har tashar Rijana zuwa Rigasa. Kwatsam bayan wuce Rijana kamar yadda bayanai su ka nuna a ranar litinin ɗin da ta gabata a sawun tafiyar jirgin na yamma, sai a ka ji fashewar nakiya da hakan ya karkatar da jirgin daga digar titinsa inda miyagun iri da ba a san adadin su da ke fako su ka buɗe wa jirgin wuta. Jami’an tsaron jirgin sun yi iya bakin ƙoƙarinsu don kawar da harin amma saboda yawan varayin na daji hakan ya sha ƙarfinsu.

Wani fasinja ya shaida mi ni cewa, jami’an tsaron sun bi shawarar masu azancin magana cewa faɗan da ya fi ƙarfin ka, ka mai da shi wasa, inda su ka kwave kayan sarki su ka saje da fararen hula. Miyagun sun fasa ƙofofin taragun jirginsu ka shiga su na kashe fasinjoji da ba la’akari da maza ko mata, yara ko manya. Ai ƙarshen mugunta kenan mugu ya zama ba ya tantance wanda ya ke son yi wa illa sai ya zama kan mai ywa da wabi. Wasu sun kwanta a ƙarƙashi ko gefen gawawwaki da hakan Allah ya hukunta su ka kuɓuta. Wasu kuma harbin ya same su amma da sauran shan ruwan su. Wannan harin dai shi ne mafi muni da ya shafi jirgin ƙasa a tarihin da zan iya tunawa a lokacin rubutun nan a arewacin Nijeriya ko ma na rage abin a kan wannan hanya ta Abuja zuwa Kaduna.
Akwai lokacin da a ka taɓa kai hari kan digar jirgin a ka lalata ta inda wani haziƙin direban jirgi ya yi dabaru cikin yardar Allah ya wuce da jirgin a wannan yanayi mai hatsari. Kazalika a farko-farkon fara jigilar sabon jirgin, an samu wani hatsari inda jirgi ya bi ta kan shanun da su ka zo tsallaka titin sa a lokacin da su ke tafiya ko kiwo. Aƙalla shanu 40 zuwa 50 su ka mutu amma babu abin da ya samu jirgin.

Da ma ai jirgi ba ya tsayawa in wani abu ya gifta ta kan titinsa. Wannan ya sa jirgin ya ke da ƙararrawa ko kuwar gaske da mutane za su ji don nesanta daga titinsa. Kazalika ai masu son kashe kan su, kan kwanta a kan digar jirgi ya zo ya markaɗe su, shikenan sai an gamu a lahira. Mutane kan ba wa duk matafiyi a wannan yanki shawarar shiga jirgin ƙasa don tsaron da ya ke da shi. Ina ganin wasu ma da sun shiga jirgin barci kan ɗauke su don kwanciyar hankali. Na taɓa shiga jirgin inda na hangi titin mota sai manyan motoci ne a lokacin ke bi. Su ɗin ma ina tunanin tarar aradu da ka su ka yi don ɓarayin nan za su iya tare kowa ko sace kowa.

Ɓarayin da sun sace sarakuna ma da ke tafiya da ’yan rakiya har da jami’an tsaro. Ba na tsammanin yanzu dai a ’yan kwanakin nan ko da an dawo da wannan jigila ta Abuja zuwa Kaduna wani zai bugi ƙirji ya ba da shawarar a shiga jirgin na ƙasa don shi ne mafi zama da tsaro.

Haka nan ba na tsammanin wanda tafiyar sa a yanzu ba ta zama ta wajibi ba zai bi hanyar nan da ta ke kimanin kilomita 200. Jirgin dai yanzu bai zama tudun-mun-tsira ba. In kun tuna farkon ƙaddamar da jirgin an riƙa rige-rigen shiga tsakanin manyan masu muƙami da talakawa.

Hakan ta kai ga in ka kwan biyu ba ka ga ɗan majalisar garin ku ba, tafi tashar jirgi za ka iya tsintarsa. Sayen tikitin jirgin ma wani babban aiki ne don akwai waɗanda ke buga waya a saya mu su tikitin ko in wani zai yi tafiya sai a sanar da wani wanda ya san mai sayar da tikiti don adana ma sa na alfarma.

Za ka je tashar ka ga ta zama kamar kasuwa. Wasu ma don amincewa da tsaron da ke tattare da jirgin har alkafura su ke yi su faɗa a tafi da su ko ba tikiti! A kan yi zaman dirsham na jiran isowar jirgin. Abin farin ciki dai matuƙar mutum ya samu tikiti to zai samu shiga jirgi. Yawanci in fasinja ya rasa tikiti yakan haƙura da tafiyar ko in akwai jirgi a gaba sai ya jira.

’Yan qalilan ne kan zaɓi shiga mota idan sun rasa jirgin. In ka ɗebe lokacin annobar Korona da a ka tanadar da jigilar jirgin, sai yanzu da a ka samu wannan akasin a ka sake dakatarwa. An yi gagarumar asara ta rayuka da dukiya. Gwamnati ko ince hukumar sufurin jiragen ƙasa ta tafka asara na yadda a ka galabaitar da wannan jirgi da kuma hakan ya tilasta dakatar da jigila. Tabbas in an yi lissafin tsayar da wannan jigila na wuni ɗaya kaɗai za a samu maƙudan kuɗi ne a ka yi asara. Kuma rashin zirga-zirgar mutane zai haddasa asara ga tattalin arziki.

Ɗaya daga fasinjojin jirgin ƙasan da ɓarayin daji su ka kai wa hari kan hanyar Abuja zuwa Kaduna Abdulwabid Ahmad ya ce bayan harin sojoji sun zo inda su ka taimaka mu su su ka hau wani tsauni gabanin jigilar su a mota zuwa tudun-mun-tsira. Sojojin sun yi hovvasa a daren su ka shigo dajin su ka yi ɗauki ba daɗi da varayin don ceto rayuwar sauran mutane da su ka maƙale a wannan bigire mai hatsarin gaske. Da alamu sojojin na cikin shirin ko-ta-kwana kan irin wannan akasin don kai daukin gaggawa.

Abdulwabid Ahmad ya bayyana cewa, bayan dasa nakiya da ta kayar da jirgin, ɓarayin sun yi musayar wuta da jami’an tsaron da ke raka jirgin, inda su ka fi ƙarfin su har su ka kutsa cikin jirgin su na harbe-harbe da kuma ya kai ga sace fasinjoji da dama. Fasinjan ya ce a ɓangaren inda ya ke an kirga mutum 9 ne su ka rasa ransu ciki har da direban jirgin, inda wasu kuma su ka samu raunuka.

Ahmad ya ce, shi ma a ƙarƙashin kujera ya ɓuya ya na addu’a har lamarin ya lafa bayan harbe wani fasinja a taragun da su ke ciki. Hakanan ya ce ɓarayin da motoci su ka zo su ka jide mutane su ka kutsa cikin daji; saɓanin yadda a ka san su da amfani da babura. Manuniya cewa ɓarayin sun shirya tsaf don kawo wannan mugun harin da haddasa asarar da za a daɗe ba a farfaɗo daga gare ta ba.

Sojoji, a cewar fasinjan, sun buƙaci fasinjojin da su kashe fitilar wayoyin su, da rage surutu har a samu a kuɓutar da su daga yankin mai hatsari.

Bayanai sun nuna cewa a lokacin da ɓarayin su ka kawo harin, su kan buɗe wuta kan duk taragun da su ka ga hasken waya har sai sun ji shiru. Munin harin shi ne ba lalle burin ɓarayin su sace jama’a ba, su na da logar jefa tsoro a zuciyar mutane ta hanyar kisan gilla da hakan zai sa a ƙara firgita da su da biyan kuɗin fansa nan take don fahimtar cewa rashin imanin na su na koyi da tsarin Fir’aunan zamanin Annabi Musa.

Kammalawa:
Jama’a na cigaba da jajantawa kan harin da ɓarayin daji su ka kai kan jirgin ƙasan fasinja da ya taso daga Abuja don kai jama’a tashar Rigasa da ke Kaduna.

In za a na bin labaru, harin ya yi sanadiyyar asarar ran fasinjoji, samun raunuka da figicin gaske, hakanan da jefa tsoro don ba a yi aunen miyagun irin za su iya kai irin wannan gagarumin harin ba. Kuma a ce har ɓarayin su fi ƙarfin jami’an tsaro da ke raka jirgin da ke da cikakkiyar damarar tinkarar barazana ko farmaki amma ba irin wannan ba.

Waɗanda su ka samu raunuka na karɓar magani a asibitin sojoji da ke Kaduna inda a ke cigaba da miƙa ta’aziyya ga ’yan uwan waɗanda su ka rasa ransu.

Shugaba Muhammadu Buhari ya ba da umurnin a tabbatar da ceto waɗanda miyagun irin su ka sace da ƙara dagewa wajen maganin ’yan bindigar.

Masifa ta shiga ƙasa da alamu ke nuna sai mutane sun dage da addu’a don neman taimakon Allah. Don duk faɗan da ya fi ƙarfin Ɗan Adam ko talaka sai ya miƙa lamuransa wajen komawa ga Allah ta hanyar gyara ɗabi’a.