Yanzu-yanzu: Aiyedatiwa na APC ya lashe zaɓen gwamnan Ondo

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Hukumar Zaɓe, INEC, ta sanar da ɗan takarar jam’iyyar APC, Gwamna Lucky Aiyedatiwa a matsayin wanda ya lashe zaɓen gwamnan Jihar Ondo.

Babban jami’in zaɓen jihar, Farfesa Olayemi Akinwunmi ya bayyana hakan a hedikwatar hukumar dake Alagbaka a Akure, babban birnin jihar.

Farfesan ya ce, Aiyedatiwa ya samu ƙuri’u 366,781 wanda hakan ya ba shi damar doke takwaransa na jam’iyyar PDP, Agboola Ajayi wanda ya samu ƙuri’u 117,845, sai kuma Adeyemi Nejo na jam’iyyar ADP da ya zo na uku da ƙuri’u 4,138.

Jaridar Alfijir ta ce ‘Daily Trust’ ta ruwaito cewa, ɗan takarar APC’n ya yi nasara ne a baki ɗaya ƙananan hukumomi 18 na jihar wanda hakan ya sa ya yi fintinkau.

Wakilin Alfijir ya ce, zaɓen wanda aka samu sayan ƙuri’u a cikinsa, an yi shi ne cikin salama duk da cewa mutane da dama ba su fito kaɗa kuri’a ba.

Aiyedatiwa ya kasance mataimaki ne ga marigayi tsohon gwamnan jihar, Oluwarotimi Akeredolu inda ya gaji mamacin a watan Disambar 2023.

By Babaji