Yanzu-yanzu: Gwamnatin Tarayya ta dakatar da shirin ƙara kuɗin rajistar WAEC da NECO bayan koken al’umma

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Gwamnatin Tarayya ta dakatar da shirinta na sauya kuɗin rajistar jarrabawar WAEC da ta NECO na 2027, har zuwa lokacin da za ta kammala shawarwari da masu ruwa da tsaki.

Rahotanni sun bayyana cewa, Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya ta sanar da matakin a wata sanarwa, inda ta ce ta janye ƙudirin wanda ke ƙunshe a wata takarda da aka fitar a ranar 18 ga Yuni da ke neman yi wa farashin rajistar jarrabawar garambawul.

A cewar ma’aikatar, an ɗauki matakin janyewar ne sakamakon samun ƙorafe-ƙorafen al’umma akan matsin da ƙarin kuɗin jarrabawar ka iya jefa su aciki.

Ma’aikatar ta bayyana cewa, da fari na ɗauki matakin ƙarin ne bisa la’akari da hauhawar farashin lamuran gudanarwa, inda ta ce an ɗauki tsawon lokaci ana amfani da tsarin farashi guda ba tare da ƙari ba duk da ƙarin adadin kuɗaɗen da ake kashewa.

Ta zayyano, tsare-tsaren tsaro, fitar da takardun jarrabawa, rarraba na’urorin fasaha, tabbatar da inganci da wasu muhimman ayyukan gudanarwar jarrabawar.

Akan haka ne Ministan Ilimi, Dakta Tunji Alausa ya umarci a dakatar da shirin bisa ƙoƙarin Gwamnatin Tarayya na damawa da al’umma da tabbatar da gaskiya da adalci wajen tsare-tsarenta a harkokin mulki.

Kazalika, ma’aikatar ta ce an ɗauki wannan mataki ne domin tabbatar da cewa an aiwatar da tsare-tsaren da suka shafi ɗalibai da iyalansu bisa la’akari da maslahar ‘yan Nijeriya.

By Babaji