Yanzu-yanzu: Tinubu ya amince da ware tiriliyan N3.3 don biyan bashin lantarki a Nijeriya

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Shugaba Bola Tinubu ya amince da wani tsari na biyan tsohon bashin Naira tiriliyan 3.3 da nufin gyara matsalar wutar lantarki a Nijeriya da akajima ana fama da ita.

A wata sanarwa da Kakakin Shugaban ƙasa Bayo Onanuga ya fitar, an ce bashin ya samo asali ne tun daga watan Fabrairun 2015 zuwa Maris 2025, kuma an amince da wannan adadi ne bayan tantancewa domin tabbatar da adalci wajen biyan sa.

Tuni aka fara aiwatar da biyan bashin, wanda kimanin kamfanonin DisCos guda 15 ne aka yi yarjejeniyar da su akan Naira tiriliyan 2.3.

Haka kuma, Gwamnatin Tarayya kawo yanzu ta haɗa biliyan N501 domin fara aiki akan al’amarin, wanda daga ciki har an biya su biliyan N223 kuma ana cigaba da biyan.

Ana sa ran wannan ci-gaba zai taimaka wajen daidaita al’amura a fannin wutar lantarki a Nijeriya musamman wajen inganta raba wuta daga DisCos da tabbatar da biya akan lokaci ga masu samar da gas, wanda babban ginshiƙi ne ga samar da ɗorewar lantarki a sassan ƙasar.

By Babaji