Yanzu-yanzu: Tinubu ya kafa kwamitin ko ta-kwana a fannin fetur

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Shugaba Bola Tinubu ya amince da kafa wani kwamitin musamman mai suna ‘Presidential Petroleum Reform & Value Optimisation Taskforce’ domin tsara sabon mataki na tsarin gyare-gyaren harkokin man fetur a Nijeriya.

A sanarwar Kakakin Shugaban ƙasa Bayo Onanuga ya fitar, an bayyana cewa tsohon shugaban banki kuma wanda ya kafa Guaranty Trust Bank, Fola Adeola shi ne zai jagoranci kwamitin a matsayin shugaba.

Wannan ya nuna shi zai riƙa kula da tafiyar da ayyukan kwamitin tare da tabbatar da an kammala aikinsa cikin lokaci.

Sauran mambobin kwamitin sun haɗa da Ademola Adeyemi-Bero, Osagie Okunbor, Abubakar Suleiman, Adaeze Aguele, Farouk Gumel, Phillipa Osakwe-Okoye da Seyi Bella, yayin da Mofoluwasho Fadayomi zai kasance sakataren kwamitin.

A cewar sanarwar, kwamitin zai yi aiki na wani takamaiman lokaci domin samar da tsare-tsaren gyare-gyare da za su ƙarfafa sauye-sauyen da ake yi a ɓangaren man fetur.

Sannan, hakan zai taimaka wajen janyo sabbin masu zuba jari da kuma ƙarfafa matsayin Nijeriya a matsayin waje mai muhimmanci wajen zuba jari a harkokin makamashi a matakin duniya.

By Babaji