Yanzu-yanzu: Amurka ta sanya ladar Dala miliyan 10 ga wanda ya fallasa inda sabon jagoran addinin Iran yake

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ta sanar da cewa za ta bayar da ladan Dala miliyan 10 ga duk wanda ya bayar da sahihan bayanai akan inda sabon jagoran addinin Iran, Mojtaba Khamenei, da Sakataren Majalisar Tsaron Ƙasa ta Iran, Ali Larijani suke.

Amurka ta ce an sanya ladan ne saboda zargin da take yi cewa shugabannin biyu na da alaƙa da ayyukan rundunar juyin juya hali ta Iran, IRGC.

Rahotanni sun bayyana cewa duk wanda ya bayar da bayanai masu amfani zai iya samun ladar kuɗi tare da kariyar tsaro da sauya masa wurin zama.

An bayar da tayin ne a ƙarƙashin shirin ma’aikatar na tabbatar da adalci, inda ta ce tana neman bayani game da wasu mutane da ya bayyana su a matsayin “shugabannin ‘yan ta’adda na Iran, kamar yadda ta bayyana ta kafar X.

“Waɗannan mutane suna jagoranci da kuma jagorantar sassa daban-daban na Rundunar Juyin Juya Halin Musulunci ta Iran (IRGC), wadda ke shirya, tsarawa da aiwatar da ayyukan ta’addanci a duk fadin duniya”, kamar yadda ta wallafa.

Waɗanda ta zayyano sun haɗa da Esmail Khatib, Ministan Leƙen Asirin Iran; Ali Asghar Hejazi, mataimakin shugaban ma’aikatan sabon jagoran addinin; Yahya Rahim Safavi, babban mai abda shawara akan harkokin soji; da kuma Eskandar Momeni, Ministan Harkokin Cikin Gida na Iran.

Sai kuma Ali Larijani, wanda shi ne Sakataren Majalisar Ƙolin Iran.

By Babaji