
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Hukumar Kula da Yanayi ta Ƙasa (NiMet), ta yi gargaɗin cewa jihohi guda 11 na arewacin Nijeriya na cikin haɗarin ɓarkewar cutar sanƙarau yayin da bushewar kakar rani ke ƙara hauhawa.
NiMet ta lissafo jihohin Sakkwato, Zamfara, Kebbi, Katsina, Kano, Jigawa, Adamawa, Gombe, Bauchi, Yobe da Borno a matsayin yankunan da ke da haɗarin kamuwa da cutar, wadda kira da Cerebrospinal Meningitis.
A cewar hukumar, sankarƙau cuta ce da kwayar Neisseria meningitidis ke haddasawa, kuma tana yaduwa ne ta hanyar numfashi musamman a wuraren cunkoson jama’a ko inda iska ba ta wadata.
Hukumar ta ce yara, matasa da mutanen da ke rayuwa a wuraren cunkoso ko masu raunin garkuwar jiki su ne suka fi fuskantar haɗari.
Daga cikin alamun cutar akwai zazzabi mai ƙarfi, matsanancin ciwon kai, ciwon wuya, amai da tashin zuciya. Najeriya dai ta sha fuskantar barkewar sankarƙau a lokuta da dama musamman a jihohin arewa.
