
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Ƙasar Iran ta bayyana cewa babu wanda ya isa ya fitar da ita daga shiga gasar Kofin duniya da za a gudanar a ƙarshen wannan shekarar.
Hakan wani mataki ne na martani da gargaɗi ga Shugaba Donald Trump na Amurka akan cewa “rayuwarsu da tsaronsu” na iya kasancewa cikin haɗari a Amurka, kamar yadda hukumomin Iran sika bayyana.
Tawagar ‘yan ƙwallon ƙafar ta Iran ta kuma bayyana a wani saƙo da ta wallafa a shafukan sada zumunta ranar Alhamis cewa, bai kamata a bar Amurka ta ɗauki baƙuncin gasar ba.
A cewarta matuƙar ba za ta iya ba da tabbacin tsaron ƙungiyoyin da za su fafata ba, ya zama wajibi a haramta mata karɓar baƙoncin gasar.
