Sojoji sun daƙile harin ‘yan ta’adda a Gadar Azir da Banki

Spread the love

Daga USMAN KAROFI

Sojojin rundunar haɗin gwiwa na Operation Haɗin Kai a yankin Arewa maso Gabas sun daƙile wani yunƙurin harin ta’addanci da aka kai kan sansanonin sojoji a Azir Bridge da kuma Banki da safiyar Juma’a, 13 ga Maris, 2026. Rundunar ta bayyana cewa ’yan ta’addan sun kai farmakin ne da nufin ƙwace sansanin, amma sojoji sun yi gaggawar tunkararsu.

A cewar sanarwar da jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, Laftanar Kanal Sani Uba, ya fitar, sojojin sun nuna ƙwarewa da shirin yaƙi inda suka ƙaddamar da hare-haren daƙile farmaki wanda ya tarwatsa tsarin ’yan ta’addan tare da tilasta musu ja da baya.

Sanarwar ta ƙara da cewa sojojin sun samu ƙarin goyon baya daga rundunar sojin sama ta Operation Haɗin Kai, wadda ta bayar da taimakon hare-haren sama kusa da wurin da aka fafata. Wannan taimako ya taka muhimmiyar rawa wajen daƙile harin tare da tilasta wa maharan tserewa daga wuraren.

Rundunar ta jaddada cewa rahotannin da ke yawo a wasu kafafen sada zumunta da ke cewa ’yan ta’adda sun ƙwace wuraren ba gaskiya ba ne. Ta tabbatar da cewa sojoji na ci gaba da rike wuraren da kuma mamaye filin daga, tare da ƙudirin ci gaba da kai hare-hare kan ’yan ta’adda domin dawo da zaman lafiya a yankin Arewa maso Gabas.

By ukarofi