Yanzu yanzu: Yadda bikin Makon Hausa ke gundana a Kwalejin Aminu Kano

Daga IBRAHIM HAMISU, a Kano

A daidai wannan lokaci ana kan gudanar da bikin Makon Hausa da Sashen Koyar da Hausa na Kwalejin Shari’a da Addinin Musulunci ta Malam Aminu Kano ya saba gudanarwa duk shekara.

Malaman kwalejin da ma takwarorinsu daga Jami’ar Bayero sun gabatar da lacca kan batutuwa daban-daban.

Sannan an samu mawaƙan zamani irin su Isah Ayagi da Salhabilun Hausa da Abdul Kafinol da sauransu, sun nishaɗantar da taron.

A kasance da Manhaja don samun cikakken rahoton bikin a fito ta Juma’a mai zuwa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *