’Yar hidimar ƙasa ta yanke jiki ta faɗi ta mutu a Kebbi 

Spread the love

Daga JAMEEL GULMA a Kebbi 

Wata matashiya ‘yar hidimar ƙasa ta yanke jiki ta faɗi a sansanin yi wa ƙasa hidima da ya ke garin ɗakingari a ƙaramar Hukumar mulki ta Suru da ke jihar Kebbi.

Matashiyar mai suna Tayachibiyacha Ebal dai ta yanke jiki ta faɗi ranar Larabar da ta gabata inda aka ɗauke ta zuwa ɗakin shan magani na sansanin horar da matasan don agajin gaggawa kafin daga bisani aka garzaya da ita zuwa asibitin tarayya (FMC) da ke Birnin Kebbi inda likitoci suka tabbatar da mutuwarta bayan ƙoƙarin da suka yi na ceto rayuwarta ya ci tura.

Kwamishinan matasa da wasanni na jihar Kebbi Alhaji Muhmmadu Fingilla ya tabbatar da faruwar lamarin inda ya ce yanzu haka dai tuni an tura da gawarta zuwa Adamawa jihar ta ta asali don iyalanta su yi mata jana’iza.

Kwamishinan, a madadin gwamnatin jihar Kebbi ya jajantawa iyalan mamaciyar tare da fatar Allah ya ba su haƙurin jure wannan rashin.

Wakilinmu ya a nemi jin ta bakin hukumar NYSC sai jami’ar hulɗa da jama’a Mrs Hadiza ba ta ce komai ba har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto.

By ukarofi