‘Yar shekara 50 a sakandare: ‘Ba a makara da neman ilimi’, cewar Atiku Abubakar

Daga BASHIR ISAH

Shade Ajayi, ‘yar shekara 50, ita ce ɗaliba mai mafi yawan shekaru a tsakanin ɗaliban makarantun jihar Kwara.

A halin da ake ciki, Shade Ajayi ɗaliba ce a Ilorin Grammar School, da ke Ilorin babban birnin Jihar.

Lamarin wannan gyatuma ya ɗauki hankali ‘yan ƙasa da dama ciki har da tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Alhaji Atiku Abubakar, ganin yadda yawan shekaru bai hana ta zuwa makaranta neman ilimi don ingata rayuwarta ba.

Kamar yadda ya wallafa a shafinsa na twita game da Shade, Alhaji Atiku Anubakar ya ce, “Tana tunatar da mu cewa ba a makara da neman ilimi.

“Ilimi shi ne mabuɗin da zai buɗe taskar tarin fasahar da Nijeriya ke da shi. Idan muka samu daidaiton ilimi, Nijeriya ma za ta daidaita.”

Atiku ya ƙara da cewa, “Kamar yadda na bada shawara a can baya, kamata ya yi gwamnati a matakin tarayya da jihohi da ƙananan hukumomi, su riƙa ware wa fannin ilimi kashi 10 cikin 100 na kasafin da sukan yi.

Shade Ajayi kan zauna a aji tare da sauran takwarorinta ɗalibai waɗanda suke tamkar ‘ya’yanta. Kuma binciken Manhaja ya gano cewa gyatumar na da sana’arta ta hannu inda bayan ta tashi daga makaranta takan ɗinka jakunkuna tana sayarwa don rufin asirin rayuwa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *