Yarabawa da al’adunsu

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Jaridar Manhaja za ta ci gaba da kawo wa masu karatu tarihi na manyan ƙabilun Nijeriya guda huɗu da suka haɗa da Yarabawa, Hausawa, Igbo da kuma Fulani cikin mako huɗu a jere.

Ƙasar Yarabawa wani yanki ce na duniya da ake samu a bigiren 6o da 9o na Arewacin Latitu (Latitude North) sannan kuma tana bigire na 2o30’ da kuma 6o30’ ta Gabas da Longitu (Longitude East).

Tana iyaka da Jihar Neja (Niger State) daga Yamma Maso Arewa. Ta Gabas kuma tana iyaka da ƙasar Jamhuriyar Bini; wato Kwatano (Benin Republic). Sai kuma Tekun Atilantika (Atlantic Ocean) da ta yi maƙwabtaka da ita ta vangaren Kudu.

Wannan ita ce asalin ƙwaryar Ƙasar Yarabawa da ta killace Jihohin Oyo, Ogun, Ondo, Legas, Osun da Ekiti waɗanda suke cikin ƙwaryar Kudu Maso-Yammacin Nijeriya, da kuma Kwara da wani yanki na Jihar Kogi da ke Tsakiyar Arewacin (North-Central) Nijeriya.

Masana harkokin al’adu na cewa duk da gauraya al’adu irin na zamani amma ba su sanya ƙabilar Yarabawa sun yi watsi da al’adunsu da suka gada tun iyaye da kakanni ba.

To sai dai da yawa daga ‘yan wannan ƙabila na cewa tsatsonsu sun fito daga wani mutum da ake kira Oduduwa har zuwa lokacin da ya kafa gari da a yanzu ake kira Ile-Ife, amma sai dai wasu daga cikinsu na ja da cewa Oduduwa shi ne mafarin tarihinsu.

Da yawa daga ƙabilar Yarabawa sun yi imani cewa tarihinsu ya faro daga fitaccen jarumi da ake kira Oduduwa wanda kuma garin Ile-Ife ke a mazauni farkon matsugunninsu.

Kuma har kwanan gobe ana yi wa Oduduwa ganin jajirtaccen bil-adama kuma fitila ga sayensu haske kuma ga tafarkin ƙabilar Yarabawa.

Yarabawa dai na da ɗumbin kayayyakin tarihi da al’adu, suna da Obatala wanda ke a matsayin ubangijinsu.

To sai dai sakamakon wanzuwar addinin Musulunci da Kiristanci da wayewa ko baƙin al’adu daga Turai, an samu raguwar kamanta Allah da wani abu da kuma tsagwaron al’adunsu na gargajiya.

Oduduwa kamar yadda masana tarihi suka nuna na cewa Lamaruzu shine mahaifin Oduduwa, kuma ya fito ne daga ƙasashen gabas har ma ake yi masa kirari da cewa Lamaruzu na yamma da Makka. Ya ƙaraso Ile-Ife da jama’arsa wajajen qarni na huɗu.

Cikin Ƙabilar Yarabawa akwai waɗanda suka yi imani cewa Oduduwa mutum ne, wasu kuwa na cewa ba shi ne tushen wannan ƙabila ba. Sai dai har kwanan gobe ana yi masa kallon uban ko mafarin duk wani da ya fito daga ƙabilar Yarabawa.

Basarake Oba Hammed Adekunle Makama, shi ne sarkin garin Olowu-Kuta mai daraja ta ɗaya a jihar Osun, haka nan kuma tsatso ne daga zuri’ar Oduduwa.

Oba Hammed yana ce, “an yarda cewa oduduwa shi ne magabatan Yarabawa. To amma kamar yadda ake cewa ya sauko daga sama da sarqa, maganar gaskiya baki bai zo ɗaya ba.”

To amma ƙasar Yarabawa akwai waɗanda ba su yarda da cewa Oduduwa shi ne magabacin Yarabawa ba kamar Sarki Atta na Ijebu-Ode, wanda ya ce, babu abin da ya haɗa su da Oduduwa.

Wasu sun ce Oduduwa ya fito daga gabas ta hanyar Yamai ta Jamhuriyar Nijar, yana tafiye-tafiye har ya zo Ile-Ife.”

Ƙabilar Yarabawa suna da jiga-jigan sarakuna kamar su Ooni na Ife da Alaafin na Oyo da Olubadan na Ibadan.
Waɗannan su ne rukunan sarakuna masu daraja ta ɗaya. Ko da yake akwai wasu daga cikinsu da ke da makamanciyar wannan sarauta amma kuma darajarsu ta bambanta.

Oba Hameed ya ƙara da cewa, “muna da wata al’ada ta gaisuwa wacce muke kira Do’baale, wanda mutum zai yi ruf da ciki ya miƙe ya yi gaisuwa a gaban sarki, wannan al’ada ce mai ban sha’awa. Mu a ƙasar Yarabawa yadda muke jaddada al’adunmu daban suke da na Arewa. Na arewacin Nijeriya addini ya fi yawa; to amma ga Yarabawa addini daban haka kuma al’ada daban. Al’adarmu ta baƙaƙen fata daban take da ta Larabawa.”

“In ba mu yi ƙoƙari ba, anan gaba duk tushenmu ma sai mun zo mun manta da su. Mu a kudu in ka ga an naɗaka kan sarauta to ana yi ne domin mu raya da jaddada al’adunmu ne,” inji shi.

Al’adun Yarabawa:
Yarabawa sun yi fice ta fuskar raya al’adu kamar a lokacin biki ko suna ko ta fuskar auratayya har ma da rabon gado.

Al’adarsu ta auratayya na zuwa da biyan sadaki, to amma kuma in namiji ko saurayi ya ga budurwar da yake so, to a maimakon ya faɗa mata kai tsaye sai ya je ya faɗa wa iyayensa domin a yi masa iso wurin iyayen budurwar. Akasari iyaye na bayar da gudunmuwa game da waɗanda ‘ya’yansu za su aura.

Dalilin haka kuwa ya zo domin kauce haɗuwa da miyagun ƙaddarori kamar na ciwon hauka ko wasu cututtuka ko tsinuwa da mai yiwuwa akwai su a cikin zuri’ar matashin ko budurwar da yake so ya aura.

Ana raye-raye da ruguntsumin raya al’adu bil-haƙƙi, sai dai a yanzu ana gauraya su da wasu tsare-tsare da zamani ya zo da su.

Sun nuna shi kansa addini wani ɓangare ne daga cikin al’adunsu, saboda haka ake la’akari da fifita al’adu kuma suke ci gaba da tasiri cikin al’amuransu na yau da kullum.

Sai dai kuma ana samun sauyi nan da can sakamakon shigowar addinin Musulunci da na Kirista da kuma shigowar Turawan mulkin mallaka a yankunansu.

Daga ina Oduduwa ya fito?
Masana tarihi kamar Dakta Muhammad Musa Maitokobi ya ce, kamar yadda bincike ya nuna Oduduwa ya fito daga ƙasashen gabashi ne sai dai ana tankiya cewa ba za yi garajen cewa wannan ƙasa ko waccar ba.

Wasu alqaluma na tarihi na nuni da cewa akwai alaƙa mai ƙarfi ta al’ada a tsakanin ƙabilar Yarabawa da Barebari musamman kan wasu al’adu da suke kamanceceniya.

“Domin kuwa shi Lamaruzu wanda shi ne uban Oduduwa, ya fito daga ƙasashen gabas ne, tarihi ya nuna tare suke da Barebari, wannan ne ya sa ake yi masa kirari cewa Lamuruzu na yamma da Makka. Hakanan kuma akwai al’adu da yawa waɗanda sun yi dai-dai da al’adunsu waɗanda ƙabilun biyu suke da kamanceceniya kamar hatta Gunda da ake maganarta ta ɓangaren Barebari, Yarabawa ma suna da ita. Akwai wani Girke na ganguna irin na su waɗanda ake kakkafasu a ƙasa, duk suna da irinsu. Suna da son juna da rashin kar na gaza, kar kuma mu bari ɗan uwanmu ya gaza sun tafi iri ɗaya. Akwai wata rijiya a nan cikin gidan sarautar Ile-Ife; tana nan da akwai sarƙa.”

“A sani na irin wannan rijiyar akwai ta a wani ƙauye da ake kira Gazargamu a tsakanin Bultuwa da Subdu da Galdiram inda yake mai tarihi. To ina ce yamma da Makka, yamma da Makka gaba ɗaya dai tun daga Maiduguri yamma da Makka ne,” inji Dakta Maitakobi.

Malam Abdulkabir Bayerabe ne, ya ce, duk da addinin Musulunci da na Kirista sun ratsa ƙabilar Yarabawa, to amma har kwanan gobe ba su yi watsi da al’adunsu ɗungurungum ba.

“Har yanzu muna gudanar da wasu al’adunmu na gargajiya, yanzu wannan gari da kake gani na Ile-Ife sun yi amanna cewa daga can ne hasken duniya yake fitowa.”

In suna bikinsu na al’ada za ka ga sun ɗauko wani mayafi fari ko harami su yafa, amma ba saboda addini ba sai domin tsafe-tsafe da sauran al’adunsu. Haka nan idan ana so a tsinewa mutum ana yi masa barazana da cewa za a faɗa wa Oduduwa ya la’ance shi, kamar ga Bayerabe domin mutum ya kiyaye.

Idan Oduduwa ya tsine ma ka tsinuwar za ta tabbata. To amma har yanzu akwai sauran al’adun na mu sai dai ba su da ƙarfi sakamakon shigowar addinin Musulunci da kuma Kiristanci da kuma shigowar baƙin al’adu na Turawa.

Al’adun mutuwa:
Ya ci gaba da cewa, “abinda ya shafi kiɗe-kiɗe da rawa na Yarabawa har kwanan gobe ana yi ba a bar su ba. Waɗannan ba a fitar da su daga cikin al’adu ba.”

“Yanzu misali a abinda ya shafi mutuwa a Jihohin Ekiti da Ondo a kan ajiye gawa domin a yi mata biki, to amma kamar anan Osun musamman a yankunan da Musulunci ya yi ƙarfi, ba mu yarda da wannan al’ada ba.”

Yarabawa mutane ne da ke biyayya ga manyansu da marabtar baƙi da kuma nuna kulawa ga jama’a. Muna mu’amala da wasu ƙabilu da kuma mabiya addinai daban-daban.

Wasu al’adu da wannan ƙabila ta yi fice a kansu sun haca da doba’le da akan yi ruf da ciki a faɗi a gaban sarki domin yin gaisuwa a gaban sarki, a yayin da mata kuwa kan tsaya bisa gwiwowinsu a ƙasa sannan su gaishe da Basarake.

Abincin Yarabawa:
A ƙasar Yarabawa ma dai ana samun Oloyes kwatankwacin fadawan sarki da ake samu a masarautun da ke arewacin Nijeriya. Abincin da aka fi saninsu da shi dai sun haɗa teba da suke kira E’ba da doya.

Yarabawa suna noma kan waɗannan cimaka, sai dai mafi yawa su ne ‘ya’yan itace- kuma akwai mafarauta a cikinsu.

A baya ana samun magidanci na aurarraki da yawa, sai dai kuma abinda addini ya zo da shi da kuma zuwan Turawan mulkin mallaka a sannu-sannu an yi watsi da wasu daga cikinsu.

Game da haihuwa kuwa duk yaron da ya ke shi ne ɗan fari akan kirashi da Dawodu a yayin da ‘ya mace ake kiranta da Bee’re.

Kaɗe-kaɗen Yarabawa:
Kaɗe-kaɗe da kuma imani da magungunan gargajiya har kwanan gobe suna yin tasiri cikin rayuwarsu. Malam AbdulKabir wanda Bayerabe ne ya gasgata fifita al’ada a wannan shiyya.

Yara daga wannan ƙabila dai ana ba su tarihin Oduduwa, wani mahaluƙi ne cikakken jarumi da ya gagari maza da dauloli. Wanda da haka ake cusawa yara koyon al’adu da tsayawa a kansu.