Ina zubar da hawaye idan na tuna matsalolin da na fuskanta a gidan aure – Hajaru Sanda

“Mata ma ‘ya’ya ne, ku ba su damar karatun boko kamar maza”

Daga AMINU AMANAWA, a Sokoto

Ba wa mata damar shiga makarantu domin neman ilimi boko kusan wani ƙalubale ne da aka daɗe ana fama da shi a Ƙasar Hausa. Da yawa akwai masu kallon bawa mata damar neman ilimin boko a matsayin lamarin da bai dace ba, bisa wasu hujjojin da suka kaɗai suka sani. Hajaru Aliyu Sanda, fitacciya a fagen gwagwarmayar kare haƙƙin bil’adama, ‘yar siyasa ce, kana kuma ‘yar kasuwa. Ta bayyanawa wakilin mu a Sokoto Aminu Amanawa, irin ƙalubalen da ta fuskanta kafin kaiwa matakin da take kai, musamman na hanata damar neman ilimin boko duk kuwa da tsananin sha’awar ilimin da take a lokacin ƙuruciya, lamarin da ke da alaƙa da yanayin da al’ummar mu ta tsinci kanta a ciki. Tattaunawa ce da ya kamata ya zama madubin dubawa ga mata, don haka ga yadda tattaunawar ta kasance:

Mai karatu zai so yaji shin wace ce Hajaru Aliyu Sanda a taƙaice, ma’ana tarihinki?
To Assalamu Alaikum. Bari in faro daga tushe. Ni dai na taso wani ‘family ko ince gida inda ba a karatun boko, wanda na dai yi karatuna na islamiyya, duk da cewa mahaifiyata ta yi boko, domin ta fito daga gidan karatun zamani kuma gidan sarauta. Saɓanin mahaifina ɗan kasuwa ne. 

A ƙalla mu da muke raye ga mahaifin mu, mu hamsin da takwas, mu mata mu ashirin da biyar. To kasancewar ni kuma tun ina ƙarama na taso Allah ya samun son karatun boko, hakan yasa na fuskanci ƙalubale masu tarin yawa. Naci da roƙo yasa aka amince in yi karatun, sai dai fa da na shi shiga, sai a fitar da ni, saboda kushe duk makarantar da aka sani. Wani lokacin sai an ɗinka uniform anyi komai, sai magana tazo cewar ba za ni makarantar ba, dalili kuwa an sanar da mahaifina makarantar ta kafirai ce, don haka ba ta dace da ‘yar musulmai ba.

Duk wannan wasan ƙwallon da ake yi da karatuna bai sa naji karatun ya fita raina ba, kuma sa’ar da naci mahaifiyata ta jajirce kan karatun, don an hanani zuwan wasu makarantun bai sare mata gwiwa ba. To kada inja ku da nisa, bayan doguwar gwagwarmaya mahaifina ya gamsu da shigata makarantar da ke kusa da mu mai suna ‘Yahayya Nawawi Islamiyya’, kasancewar islamiyyar nan da a ke cewa shiyasa Babana ya amince.

Duk da cewa jinkirin da nayi na shiga boko naƙasu ne gare ni, kasancewar waina (tsarana) sun wuce ni, sai dai alhamdu lillah, domin Allah ya share hawaye na ta hanyar bani kaifin ƙwaƙwalwa mai saurin ɗaukar karatu.
Ba zan mantaba, tun shigata makarantar duk akayi jarabawar Ni ke ɗaukar ‘first position’, wannan ne fa ya zama silar da malamai na suka duba girmana na kasancewar na shigo a makare, suka ce tunda ina da ƙoƙari sosai mai zai hana a ɗaga Ni sama don in samu damar cimma tsarana, da kansu suka yi wannan hukuncin ba tare da gida an roƙe su ba. Wannan ne yasa ban kammala aji biyar ba, ban kuma yi shida ba na wuce ajin farko a sakandare.

Na fara ajin farko a ‘Nana girls secondary school’. To fa a daidai nan da nake tunanin na sha, duk wani ƙalubale yayi wucewa, kwatsam a wata rana mahaifina yazo da almakashi yana neman uniform ɗina zai yayanka su, wanda hakan na nufin bai amince da makarantar da nake zuwa ba, duk da cewa ta mata zalla ce. Ba zan manta ba, lokacin mahaifiyata na shirin zuwa aikin hajji, hakan yasa na shiga fargaba, idan ta tafi kenan ba Ni ba boko sai ta dawo. Daga ƙarshe dai shawara ta zo mana, aka nema min wata makarantar mai suna Hafsatu Amadu Bello model & Arabic secondry school. Ba tare da sanin Mahaifin nawa ba aka ɗinka min kayan makaranta tare da yi min siyaya na fara zuwa. Duk da cewa muna da tunanin idan ya sani ba zai hana ba, don makaranta ce da ba waɗanda ba musulmai ba ko ɗaya.

To fa lokacin da na dawo hutu, na haɗu da baban namu fa sai ya hau ni da faɗa. Tare da tabbatar min ya fitar da ni makarantar. A nan dai na fahimci cewa bokon ne har yanzu bai gama amincewa da shi ba. Haka dai na yi ta zaman, idan hutu yayi in lallaɓa in koma, idan na dawo ya ta min faɗa. Idan na dawo gida a hanani ko ƙofar gida in tafi. Sha’ani da gidan yawa sai a tai zuga Baba suna cewa, ya za ayi yana da ‘ya’ya mata fiye da ashirin, duk basu yi boko ba, ace ita a barta ta yi. 

Bari in ɗan katse ki kaɗan. Shin wannan tsarin na rashin karatu al’ada ce ta wannan Unguwa taku mata basa karatun boko a wannan lokacin?
Eh to, ba zance ba a yi ba, domin akwai gidaje da dama da ‘ya’ya mata ke zuwa karatu, domin makarantar mu cike take da ɗalibai mata, sai dai wannan ina zancen ne kan namu ‘family’ sam ba a son karatun na boko, kuma bansan meyasa ba. Kuma ba wanda ya bani ƙwaƙwaran hujja, abin da kawai ‘yan’uwana ke ta nanatawa shi ne, ba wadda ta yi a gidan don haka bai kamata na yi ba. Duk da wannan matsalar bai hanani yin suna a makarantar tamu ba, don tun daga gate har ƙarshen makarantar ba wanda bai sanni ba, sanadiyyar ƙoƙarina, duk wani abu da za a yi na gasa zai yi wahala ban zo na ɗaya ba.

Halin da nake shiga idan ance an yi hutu yasa malamanmu gano akwai matsala, domin za ka ga kowa na murnar komawa gida ban da Ni. A cikin irin wannan yanayi na kammala aji ɗaya, na shiga biyu. To fa nan zancen aure ya kunno kai. Domin a gidanmu har ‘yan shekaru tara an aurar.

A haka na yi aji uku ko shi kuwa da siɗin goshi. Zance na gaskiya na jima ina son naje ‘private school’ saboda ina so nima in iya Turanci, domin sanin kowa ne makarantun gwamnati musamman ma a Sakkwato ana dai yi ne kawai. Idan har kana son ingantaccen karatu to fa sai dai a makarantun kuɗi. A taƙaice dai ina aji biyar zancen aure ya taso. An haɗa ni da wani, ba don na so yin auren ba, saboda hankali na kan karatu yake. Saboda ina da buri mai yawa da na ɗora kan samun ilimi mai zurfi.

Misali tun ina ƙarama nake da dogon tunani a sha’ani na siyasa, ina hango irin canje-canjen da ya kamata zaɓaɓɓun ‘yan siyar mu su kawo. Ina da tabbacin ta hanyar ilimi ne kawai zan iya samun bada gudummawata, hakan na nufin amayar da ra’ayoyina wanda na ke burin su samu karɓuwa.
 
Kenan ki na so kice mana ba auren soyayya ki ka yi ba?
Ba auren soyayya ba, domin duk shagalin neman ina makaranta aka yi, asalima ko Ni a makaranta aka kawo min shi na ganshi. Kasancewar yawan matsin lamba da nake samu kan zancen aure yasa da ƙanin babana yazo tambayar ko ina son sa, na ce, su je su yi bincike, idan sun aminta da halayensa, to na amince. Ina can aka kai sadaki, lefe har ma saka rana. Don haka ina dawowa aka ɗaura aure. Wata ɗaya bayan auren na samu mummunan hatsari ni da ƙanwata, wanda da ƙyar na sha. To fa a nan komai ya canza, domin ba jimawa da hakan ya ƙaro aure. Bayan samun sauqi na ɗan koma makaranta, to kuma abin bai samu muhallin zama ba, duk da na yi naci matuƙa.

Maigidan bai barki komawa karatun ba ne?
Idan na ce haka gaskiya nayi ƙarya, makarantar da na fara shiga a Kano shi ya sani, da muka dawo Sakkwato ne yace bazai iya ɗaukar nauyin karatun ba, amma ya amince idan zan iya. To a lokacin bani da wata sana’a da nake yi, wanda hakan ya zama tsaiko ga karatun nawa. Sai na fara ɗan sede-sede, nice yin fanke, siyar da omo da gishiri, kai har ƙanƙarar zaƙi sai da nayi duk da cewa bani da firijin a lokacin, hakan bai hana ni ba. Zan ƙulla in bada a fitarmun da shi waje a seda, a kawo mani kuɗin, duk don in samu abin da zan ɗauki nauyin karatuna.

A cikin irin wannan yanayi na haihu. Zaman auren dai yazama sai a hankali. Rashin daɗinsa yafi daɗin yawa. A wannan lokacin ne nayi nazari kan ɗaga sana’ata zuwa mataki na gaba. Domin yana da kyau mata su laƙanci matakan sana’a, idan baki da kuɗi, kada ki ce sai kin samu kuɗi mai yawa za ki yi sana’a, hakan zai sa ki fara samun wulaƙacin maigida, ko ki zama maroƙiya da mutane za su fara gudun ki, idan kina da kishiya ma haushi ya kashe ki. Da kaɗan da ki ke da shi samu sana’a komai ƙanƙantar ta ki fara. Lokacin da ta bunƙasa, kada kice za ki dawamma a ƙaramar sana’a matuƙar akwai yadda za ki mayar da ita babba. Ko da sana’a iri ɗaya za ki yi, ki tabbatar tana bunƙasa kina ƙara yawan ta. Misali, kina siyo omo loka-loka ki ƙulla, sai ki ka tara kuɗin da za ki iya siyen buhu, kada kice dole loka ce za ki ci gaba da siya, ba za ki haɓaka riban ba.

A lokacin na fahimci babu shagunan da ake siyar da kayan haɗa fanta a garin namu na Yabo, sai an je Sakkwato. Don haka sai na haɗa kuɗaɗena na bada aka kawo min ina saidawa. Idan na haɗa sai inje Sakkwato in saro. Bazan mantaba, asibitin da nake zuwa ganin likita sakamakon hatsarin da na gaya maka na yi wanda har zuwa wannan lokacin ina tare da matsalar da ya bar min. A wurin na saba da wata ‘nurse’ wadda ta sanadiyyar ta na fara adashi. Kada in jaka da nisa ta wannan sana’a na koma makarantar da na fara zuwa wato Nana girls. Na koma bana wuni birni, bani kwana qauye, tsakanin Sakkwato da Yabo. Na fuskanci matsaloli da dama da suka sa har na samu cikin ɗana na biyu ban kammala babbar makaranta ba. Hakan bai sa gwiwata ta yi sanyi ba a kan burina.

A wannan yanayin ne zaman auren nawa ya ƙare, na dawo gida. To fa nan Ungulu ta koma gidanta na tsamiya. Wato bayan komai ya daidaita na koma makarantar da na bari wato Hafsatu. A nan na kammala karatun sakandare. Kuma zan tabbatar ma na rubuta NECO haihuwa ko yau ko gobe. Kuma cikin yardar Ubangiji ba darasin da ban samu ‘credit’ ba.

Bayan wani lokaci na shiga poly nan Sakkwato, inda karatu na nisa sai kuma matsala dai irin ta baya ta sake dawowa, karatun ya tsaya. Na yi JAMB har zan fara karatu a nan Ɗan Fodiyo wato UDUTH, na sake samun matsala a gida, a wannan karon sai na zauna a gida na sawa sarautar Allah ido, amma fa ba hakan na nufin zuciyata ta haƙura ba.

Matsalolin gida da suka yi min yawa yasa na fara neman matsera, tunanina ya tsaya cak kan mafita ɗaya, wato dai aure. Domin shi kaɗai ne zai fitar da ni daga gidanmu. Wannan yasa na daina kallon wa yakamata in aura, na koma kallon wa zai zo ya aureni. Hakan ne babban kuskuren da nayi, domin shi ne silar zaɓen tumun dare da nayi. Na yi auren, amma sai yazama tamkar fita daga ruwan zafi ka faɗa wuta. Matsalar da na samu kaina a gidan auren nan har yau idan na tuna wasu sai na zubar da hawaye. Wannan kuwa ba komai yasa ba face takurar gida. Na san wannan ƙaddara ce, amma komai na da sila. Don haka ba zan gushe ba face na yi kira ga iyaye, ‘ya’ya mata ma ‘ya’ya ne, ku ba su damar yin karatun boko kamar yadda ku ka bawa maza. 

Wannan auren ne dai ya zama silar samun sassauci da nayi a gida, domin bayan dawowata, ma’ana auren ya mutu, sakamakon irin azabar da na shi, kuma zance ya bayyana, ga kuma wahalar da ta nuna kanta a jikina ya sanya mahaifina tausaya min matuƙa. Wannan ne ya sa aka ɗan sakar min mara in ɗan fitsara.

Sai dai na fito da ciki, wanda hakan yasa na samu matsaloli na renon ciki da kuma waɗanda ba a rasa ba. Allah cikin ikonsa na haihu lafiya, sai dai yaron ya fara ciwo. Tsayin lokaci ina fama kafin mu gane yana tare da cutar sikila. Muka shiga tarangahuma, daga ni sai mahaifiya ta, sai kuma wasu daga ‘yan’uwana, domin tun haihuwarsa zuwa yanzu da nake firar nan da kai shekaru tara kenan, mahaifinsa gani biyu kawai ya yi masa.

Kada in jaka a zancen da tsayi, bayan ɗan lokaci na sake kakaɓe burina na karatu na fito da shi, idan nace ma nayi karatu cikin kwanciyar hankali kamar ko wace ɗaliba na ma ƙarya, domin kamar yadda nayi shege da fice tsakanin makarantun sakandare haka nayi a wannan lokacin, wanda duk wanda bai san halin da nake ciki a gida ba sai ya ɗauka bana son karatun ne, ganin sai karatun ya kankama sai a nemeni a rasa.

Bazan manta inda sauƙi ya shigo ba, ‘former minister’ Aisha Abubakar wadda ta kasance ‘yar’uwata, kuma kowa ya san mun shaƙu da ita, ta yanda ko jimawa tayi bata ganni ba za ta zo har gidanmu, ma’ana tabi sawu na. Kuma mahaifina ya aminta da ita. Don haka na fara samun damar zuwa wurinta a Abuja da take zaune. Daga nan ne fa na nemi ‘admission’ a Benin republic, Kwatano, a nan nayi karatuna, wanda na yi digiri a fannin ‘environment management science’. Amma fa da zumar zuwa Abuja nake karatun. 

Bayan na kammala, na zo na yi bautar ƙasa cikin nasara. Yanzu haka na koma ABU Zaria, ina postgraduate diploma, wanda yanzu haka ban kammala ba.

Yanzu haka mahaifin nawa Allah ya masa rasuwa. Kuma abin farin ciki, kafin rasuwarsa komai ya yi kyau tsakanin mu, kuma har qarshen zamansa duniya yana samun albarka, tare da yimun fatan alkhairi a rayuwata. Fatana Allah ya mashi rahma, yasa ya huta. Duk da ababen da suka faru, Baba Uba ne da ke tsaye ga iyalansa, kuma ina sonshi sosai.

To, Allah ya yi masa rahman. Daga nan kuma ina aka dosa; aiki ne ko kuma gwagwarmayar ce?
Eh to, zan iya cewa kusan a haɗe nake tafiya da su. Domin ina aiki ‘organization’ da dama. Bayan ayyukan da muke yi tare da minista wanda da yawa aikin jinƙai ne, ina cikin ‘police community releted committee’, ina cikin ‘National exco’, haka zalika nice ‘Women coordinator’ ta ‘Human right network’. Daidai gwargwado muna bada gudummawa wurin kare haƙƙin ɗan’Adam, musamman mata da aka ciwa zarafi ta hanyar fyaɗe da sauransu. Har wa yau, nayi aiki da ‘National social investment office’. Kuma yanzu maganar da nake ma na samu aiki, zan fara da yardar Allah.

Na’am! To baya ga irin ƙalubalen da a ka fuskanta, waɗanne irin nasarori ne a ka samu a rayuwa?
To alhamdulillah. Nasara ta farko zance ɓangaren sana’o’i ce. Nayi sana’o’i da dama, kuma yanzu na fara girbar wahalata, domin na san mutane da dama, na samu alkhairai masu yawa, yanzu haka da nake magana da kai an min ‘north-west coordinator’ ta ‘noodles young ambassador’.

Na samu ɗaukaka daidai gwargwado, ina taimakawa mata ‘yan uwana ta hanyar koya masu sana’o’in hannu. Ina da kamfani nawa na kaina da muke gudanar da harkokin mu na samu mai suna ‘Hajas multi business Nigeria limited’. Sannan muna da kamfani na haɗaka da wata barista, wanda nan da ba da jimawa ba zamu gabatar da wani aiki na musamman.

Babbar nasara kuwa shi ne iya kula da ‘ya’yana tare da ba su ingantaccen ilimi, ba tare da naje nayi ƙaramar murya ba. Na samu hanyar da nake kula da buƙatuna da na ‘ya’yana ba tare da na roƙi kowa ba. Wannan nake kallo a matsayin babbar nasara.

Kamar yadda muka sani, rashin bawa ‘ya’ya mata damar yin karatu mai zurfi shine abin da ke ci wa al’ummar Hausa tuwo a ƙwarya, musamman ma a nan Sakkwato. Wacce shawara za ki bada ta yadda za a haɓaka ilimin ‘ya’ya mata?
To, shawarar da zan ba musamman ga iyaye, ya kamata a ce su gane cewa, lokaci ya canja, zamani ya zo da sauyi da ya shafi rayuwar mata. Kuma su dinga yi suna tuna cewa, mata ne iyayen tarbiyya, da ilimin da mace ta samu ne zata tarbiyyantar da ‘ya’yanta. Idan mace na da ilmi kai miji akwai ababe da dama da zaka huta da yinsu. Misali ‘home work’ na yaranka. Kaga idan bata da ilmi sai dai kai kayi, ko ka ɗauki wani ka biya shi kuɗi ya yi masu. Kuma tarbiyyar mai ilmi bata taɓa zama ɗai da ta jahila.

Hajiya Hajaru

Sannan ina kira ga shuwagabannin mu, don suma nauyi ne kansu. Domin kai wakili ne, kuma zai yi kyau ka zamo wakili na gari, ta hanyar ganin ka jajirce wurin ganin an bawa ‘ya’ya mata haƙƙinsu kamar yadda ake baiwa maza ta fuskar ilmi.

Shuwagabanni su naɗa wakilai da za su zaƙulo ire-iren waɗanan iyaye, a wayar masu da kai, idan babu halin karatun ne a taimaka masu da hanya mai sauƙi da za su bai wa ‘ya’yansu ilmi. Jahilci ne kesa ana kallon boko a matsayin hanyar lalacewa. Ko wane tsuntsu kukan gidansu yake yi. Tarbiyyar da ka bawa ‘ya’yanka ce za ta nuna masu hanyar bi yayin neman ilimi. Ma’ana mai kyau ko akasin haka.

To, ko Hajiya Hajaru na da ra’ayin yin takara?
Ƙwarai da gaske kuwa. Matsalar rayuwa da na shiga ta samun sha’awar takara, don taimakawa waɗanda ke fuskantar irin tawa matsala a yanzu. Ina da burin samun kujerar mulki don in samu ƙarfin da zan tsaya wa matan Jihar Sokoto. In zama mai share kukansu daga tauye haƙƙin da ake masu a gidajensu, da kuma cin zarafin da ake masu a cikin al’umma, kamar fyaɗe, wulaƙacin da suke fuskanta a gidan aure, da sauransu.

Sannan ina da burin ganin na wayar da kan iyaye kan ilimin ‘ya’ya mata, sannan samar da sana’o’in hannu ga matasa, domin da yawa daga cikin matsalolin da suke faruwa a gidan aure rashin sana’a ke haddasa su. Za ka ga saurayi na tasawa sai a har-haɗa ayi masa aure, ba tare da tabbatar da yana da tsayayyar sana’a ba, to ya ko ba za a samu matsala a auren ba. To duk waɗannan canjin zasu samu ne idan ina da wani ƙarfi a gwamnati. Don haka da yardar mai duka Allah a zaɓe mai zuwa 2023 zan fito takarar.
  
Kenan fitowar takarar da za ki yi na kai ‘yanci ga matan da al’ummar ke yi wa kallon marar gata ne?
Eh to, ba zan yi ƙarya ba, wannan ne babban ƙudurina, domin shine silar sha’awar siyaya, kasan ance ciwon ‘ya mace na ‘yar’uwarta mace ce. Kuma ba wanda yasan zafin tauye haƙƙi kamar wadda aka tauye wa. Sai dai duk da haka ba yana nufin shi kaɗai ne ƙudurina, ina tausaya wa rayuwar da matasan mu na wannan lokaci ke yi.

Wahalar da suke sha a ƙoƙarin samun na bawa cikinsu haƙƙinsa. Kaso mai dama na ta’addancin da matasa ke yi rashi ne ke jefa su a ciki. Don haka idan an sawwaƙa rayuwa ga matashi, mace ta samu ilimin bawa ‘ya’ya tarbiyya, kuma al’umma ta girmama darajar Mata, to tabbas za a samu zaman lafiya a tsakaninmu.

Wacce shawara za ki ba wa mata masu zaman kashe wando?
To, duk da ana ta yaƙin nema maku (mata) ‘yanci da sauƙaƙe rayuwa, idan fa ba ku miƙe ku ka nema ba ba ta inda za ku more rayuwar. Domin idan ki ka ce daga kwance ki ke jira gwamnati ta kawo maki har bisa gado to kin faɗa wa kanki ƙarya. An ce dai babu Maraya sai raggo, idan ki ka zauna, ba abin da zai sa ba za ki ga zaunau ba. Duk halin da ki ke kai a gidan aure ba zai hana ki sana’a ba. Idan baki fita kiyi ‘yan sede-seden da za a shigo cikin gida a siya.

Ga yanda zamani ya sauwaƙa mana kasuwanci, ta hanyar kafafen sada zumunta ma sai ki siya, ki siyar. Idan kuma ba ki da jari mai yawa, sai ki fara da kaɗan kamar yadda na faro. Idan ma babu gabaxaya sai ki yi sana’a da qarfin jikinki. Duk inda ba sana’a za ka tarar da gulmace-gulmace da hasada a wurin. Don haka mata ku kama sana’a yafi, domin ita ce ƙima, daraja tare da kwanciyar hankalin ku.

To, mu na godiya sosai.
Ni ma na gode ƙwarai.