Numfashin mutum

Daga MUSTAPHA IBRAHIM ABDULLAHI

’Yan uwa masu karatu, assalam aliakum. Barkanmu da wannan lokaci, barkan mu da sake saduwa a wannan shafi mai albarka da ke kawo muku bayanai game da jikin ɗan Adam, domin ku fa’idantu, kusan yadda jikin ku ke aiki.

Rubutun yau zai mayar da hankali kan wani babban al’amari da ɗan Adam ke yi kulla- yaumin ba tare da ya kula da shi ba. Ku dai kawai ku biyo ni. 

Jiki na da naka, da naki, yana gudanar da al’amuran yau da kullum masu tarin yawa, waɗanda da zamu zauna domin mu ƙididdige su, sai dai musha wahala kawai, domin kuwa ba zamu iya ba. Wannan shi yasa malaman kimiyya suke yin hasashe a cikin al’amura da dama da suka shafi rayuwar mu, saboda ƙididdiga ba za ta yi aiki ba.

Yau, a cikin ikon Rabbani, zan ɗauki daya daga cikin muhimman al’amuran da jikin ke gudanarwa, tun lokacin da ni da ke, da kai muka zo duniya, har ya zuwa ranar da kwanan mu zai ƙare. Wannan al’amari da jiki ke gudanarwa babu ruwan sa da minti ko sakwan, ko awa; babu ruwan sa da girman ka, ko ƙanƙantar ka, ko matsayin ka, ko ko muƙamin ka; babu ruwan sa da wane irin yanayi ake ciki: zafi, sanyi, damina, ko wanin su; matuƙar dai mutum yana raye, to wannan al’amari zai gudana. Wannan al’amari ba komai bane illa –NUMFASHI! 

Numfashi na ɗaya daga cikin abubuwan da bamu fiye damuwa da su ba, saboda kawai mun saba da dinsa, juma min sakankance mun samu yaƙinin cewa zai faru, ba tare da daddagewa daga ɓangarenmu ba domin gudanar da shi. Abu ne kamar mai sarrafa kansa, wato “automatic” inji nature.

Numfashi yana daya daga cikin abubuwan da ke nuna cewa mutum yana raye, bai mutu ba; kuma yana canzawa dangane da yanayin da mutum ya tsinci kan sa a ciki; kamar lokacin nutsuwa, da lokacin firgici, da lokacin zulumi. Za mu ga abubuwan da ke canja dabi’ar numfashi a lokuta daban-daban a rubututtukan gaba masu zuwa da Yardar Mai kowa. Mafi yawan abin da zai zo ranki/ ranka idan anyi maganar numfashi, shi ne shaqar iska, gami da fitar da ita. E, hakane, amma a takaice kenan, saboda bayanin numfashi a warware, ya fi gaban haka!

A duk minti guda, kana numfasawa sau 17 zuwa sau 20. Wannan idan kana/kina cikin halin kwanciyar hankali kenan. Muna shakar iskar oksijin (O2), sannan mu fitar da ta kabon dai ogzayid (CO2). Ita iskar O2, da ita kwayoyin halitar jikin mu suke amfani domin su gudanar da ayyukan daban-daban. Ita kuwa iskar CO2, ita ce a matsayin datti ko daudar da kwayoyi halitta ke samarwa a yau da kullum, kuma tana bukatar a fitar da ita daga jiki, idan ba haka ba, taa cutar dashi.

Cikin ikon Sarkin halitta, muna musayar iska ne taskanin mu da tsirrai. Iskar da muke fitarwa CO2, ita suke bukata, sannan kuma iskar da muke bukata (O2), ita tsirrai ke fitar wa. Ta haka ne muke musayar iska tsakaninmu da su. Wani aikin sai Rabbani!

Haƙiƙa iska tana dauke da gamayyar sinadarai daban-daban. Shin ko kun san al’amuran da ke faruwa yayin da kuka sheki iskar oksijin, sannan kuka fitar da marar kyau, wato iskar kabon dai ogzayid? Abubuwa ne daki-daki, masu dogwayen bayanai; amma zan iya ƙoƙari na wajen taƙaice muku su, ta hanyar da za a samu saukin ganewa.

Numfashi ba zai faru ba, har sai wasu jiga-jigan ko muhimman abubuwa sun hadu. Waɗannan jiga-jigai su ne:

Bangon ƙirji, wanda ke ɗauke da kasusuwan haƙarƙari, tsokar nama, hanyoyin jini, da jijiyoyin motsi.

Shamakin tsoka da ya raba tsakanin kogon ƙirji da kuma kogon ciki, wanda a turance ake kira da “diaphragm.” tare da jijiyoyin motsin sa da hanyoyin jinin sa.

Huhu tare da jijiyoyin motsin sa da hanyoyin jinin sa. Cibiyoyin kula da numfashi wadanda suke da tasha a kwakwalwa da kuma laƙa.

Kowanne daga cikin abubuwan da na lissafa yana taka muhimmiyar rawa a lokacin numfashi., wanda da za’a rasa ɗaya, numfashi zai yi wahala. Bangon kirji yana taimakawa wajen budewa yayin da huhu ya cika da iska, da kuma tsukewa yayin da iska ta fita daga cikin huhu. Shi kuma shamakin da ke tsakanin kogon ciki da na ƙirji, yana ƙara girman kogon ƙirji yayin da ka shaƙi iska, sannan kuma yana rage girman kogon ƙirji yayin da ka fitar da iska waje daga cikin huhu.

Huhu a turance, shi ake kira da “Lungs”. Kowanne lafiyayyen bil adama, yana da huhu guda biyu, dama da hagu. Huhu shi ne dakin da iska ke shige-da-fice a yayin da mutum yake numfashi. Tsakanin huhun dama da na hagu, wato a tsakiyar su, akwai bututun iska wato trachea. Asalin bututun iska ya fara ne daga kofofin hanci, zuwa kogon hanci, ya bi ta makogwaro, har izuwa inda zai rabu gida biyu: daya zai dama, domin ya shiga huhun dama, dayan kuma zai yi hagu domin ya shiga cikin huhun hagu.

Da zarar bututun iska ya shiga cikin huhun dama dana hagu, sai kowanne daga ciki ya fara rassa, yana kuma kara sauka cikin huhun.  Zai yi ta yin waɗannan rassa irin na bishiya yana yin kasa, har ya tiƙe a matsayin “buhun musayar iska” wanda a nan ne a ke musayar iskar da ta shiga huhu, da kuma iskar da za a fito da ita daga huhun.

Buhun musayar iska baya kama da irin buhun da kuka sani, idan zan iya wassafa muku shi, sai in ce yana yanayi da balan-balan ko ince balo. Buhun  musaayar iska ‘yan ƙanana ne matuƙa. Bari in baku misalign yadda buhun musayar iska yake. Mu ƙaddara ka samu balan-balan kamar guda biyar haka, ka ɗan hura su kaɗan, sannan ka ƙulle bakin kowacce balo. Daga bisani ka ƙulle waɗannan guda biyar din a jikin ɗan siririn ice ko gamba haka. Balo guda biyar din su ne a matsayin buhun musayar iska; gambar kuma it ace a matsayin reshen karshe na bututun iska, wanda a turance ake kira da “respiratory bronchiole.”

Masana sun ƙiyasta cewa da za a tsattsaga kowanne buhun musayar iska a jera su kusa-da-kusa, to da sun kai misalin girman filin wasa na ƙwallon ‘tennis’. Kunga kenan akwai hikima wajen tattare su waje guda domin su karvi iska ma tarin yawa. 

Tun lokacin da mutum yake ciki bututun iska da zarar ya shiga cikin huhu sai ya yi ta rassa kamar na bishiya, wannan shi yasa ake ce masa “tracheobronchial tree; sai dai shi rassan sa kasa suke yi, ba sama ba. A wannan lokaci na rayuwa a cikin uwa, da akwai wasu sinadarai masu hana bututun iska wato trachea, yin rassa tun kafin ya shiga cikin huhu. Tun daga maƙogwaro har zuwa tsakiyar kirji, waɗannan sinadarai basa bari a samu rassa. Bututun iska shi ne ya dangane izuwa kogon hanci. Haka kuma daga ƙasan bututun iska, da zarar ya shiga cikin huhun dama da na hagu, wasu sinadaran ne ke sanya su su yi ta rassa har izuwa ƙarshe.

Allah ya halicci huhun mutum daga wasu kwayoyin halitta na musamman  masu taushi da laushi, kuma yana iya talewa da tsukewa, wato dai kamar yadda zaka ja danƙo ko kyauro ka taɓe shi, idan ka shika ya koma yadda yake, suma haka suke. Wannan shi yasa huhu yake iya buɗewa ya kumburo yayin da iska ta shiga cikin sa, sannan kuma ya tsuke yayin da iska ta fita daga cikin sa.

Ina ga zai yi kyau a ce mun kalli halittun da suke ta’ammuli da numfashi kafin mu je ga yadda shi kan sa numfashin yake gudana. Wannan shi yasa na tsaya dogon bayani akan yadda halittar huhu take, tare da bututun iska. Yanzu zan dora ƙarashen bayani akan huhu, daga bisani kuma mu ga yadda kogon kirji yake tallafa wa numfashi.

Huhun mutum na dama da na hagu, sun sanya zuciyat ɗan adam a tsakiya. Saboda hikima da fikra ta Sarkin halitta, hakan na da wani sirri da zai tabbatar da kasancewar mutum a raye. Zuciya tana harba jini mai dauke da iskar CO2 , ciki huhu, inda a nan ne za a cire ta daga cikin jinin sannan a zuba iskar oksisjin. Jinin yana bi ne ta ta hanyoyin jinin da suka tashi kai tsaye daga zuciya zuwa cikin huhu, ana kiran su da “pulmonary arteries”.

Bayan an sanya wa jinin iskar Oksijin, an kwashe iska marar kyau , jinin zai biyo ta wasu hanyoyin jinin daga huhu, ya dawo zuciya, ana a ce musu “pulmonary eins.”

Ku tara a sati mai zuwa da yardar Sarkin halitta domin ci gaba. Kafin nan na ke cewa, wassalamu alaikum.