Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Gwamnan Jihar Neja, Umaru Bago, ya ce yara maza na barin makarantun sakandaren matakin JSS a faɗin jihar domin shiga aikin haƙar ma’adinai, saboda suna ganin aikin ya fi kawo kuɗi fiye da karatu.
Bago ya bayyana hakan ne yayin wata hira da shirin Sunday Politics na gidan talabijin na Channels, inda ya bayyana haƙar ma’adinai a matsayin babbar matsala a jihar.
Jawabin gwamnan ya zo ne a daidai lokacin da ake ta cece-kuce kan mutuwar mutane 37 da ake zargi da haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba, waɗanda suka mutu a hannun Hukumar Tsaro da Kare Fararen Hula ta Nijeriya (NSCDC).
Mutanen na daga cikin ɗaruruwan waɗanda aka kama yayin wasu samame da aka gudanar a ranakun 15 da 16 ga Satumba a yankin Estate na Laftanar Janar Mohammed Inuwa Wushishi da ke Minna, babban birnin Jihar Neja.
Bayan faruwar lamarin, gwamnatin tarayya ta dakatar da Kwamandan NSCDC na Jihar Neja, Suberu Aniviye, tare da wasu jami’an hukumar, yayin da aka bayar da umarnin gudanar da bincike domin gano musabbabin mutuwar mutanen. Daga bisani, NSCDC ta ce jami’anta 24 suna tsare bisa alaƙa da lamarin.
Bago ya ce, wani rahoto da Asusun Tallafa wa Yara na Majalisar Cinkin Duniya (UNICEF) ya fitar kan Shiroro da wasu ƙananan hukumomi a jihar ya yi hasashen cewa nan da shekarar 2027, ba za a samu ko yaro namiji ɗaya a ajin JSS2 ba saboda yadda yara ke komawa aikin haƙar ma’adinai.
“Mun san cewa haƙar zinare a Jihar Neja ta zama wata ɗabi’a da aka saba da ita,” inji shi. “Rahoton UNICEF kan Shiroro da sauran ƙananan hukumomi ya ce nan da 2027, ba za a samu ko yaro namiji ɗaya a Grade 8, wato JSS2, da Grade 7 ba, saboda duk sun shiga aikin haƙar ma’adinai na gargajiya. Sun bar azuzuwa kuma ba sa zuwa makaranta. Wannan matsala ce a gare mu.”
Gwamnan ya ce, magance matsalar na da wahala saboda gwamnatin jihar ba ta da cikakken iko kai tsaye kan hukumomin tsaro, don haka ba za ta iya ba da umarnin kama masu haƙar ma’adinai ko gudanar da wasu samame ba tare da haɗin gwiwar hukumomin da abin ya shafa ba.
Ya ce, da dama daga cikin yaran ba sa son komawa makaranta bayan sun ga irin kuɗin da suke samu daga aikin haƙar ma’adinai. “Amma waɗannan mutane, saboda sun ɗanɗana kuɗin haƙar ma’adinai, ba za su iya barin wurin ba,” inji Bago.
Gwamnan ya ce akwai buƙatar ɗaukar mataki mai ƙarfi domin daƙile lamarin, ciki har da samar da umarnin zartarwa daga Fadar Shugaban ƙasa da Ma’aikatar Ma’adinai domin hana haƙar ma’adinai a wasu wuraren da aka gano cewa ayyukan na haifar da matsala. “Da zarar an yi hakan, za a iya aiwatar da shi,” inji shi.
Bago ya kuma koka kan yadda mazauna wasu yankunan da aka fi sani da noma suka koma aikin haƙar ma’adinai. Ya kawo Shiroro a matsayin misali, yana mai cewa yankin ya kasance ɗaya daga cikin ƙananan hukumomin da suka fi dogaro da noma, kafin mazauna yankin su bar aikin noma su koma haƙar ma’adinai na gargajiya.
“Adadin ƙoƙarin da suke zubawa a wannan aikin haƙar ma’adinai, da sun mayar da rabinsa wajen noma, da sun fi samun ci gaba,” inji shi. “Shiroro ya kasance ɗaya daga cikin manyan ƙananan hukumomin da suka fi dogaro da noma, amma sun bar noma sun koma haƙar ma’adinai. Wannan babbar matsala ce, kuma dole ne a ɗauki mataki na musamman.”
Yayin da aka tambaye shi ko gwamnatinsa za ta ɗauki tsauraran matakai kan iyayen da ke barin ’ya’yansu su daina zuwa makaranta domin shiga aikin haƙar ma’adinai, Bago ya ce gwamnati za ta duba yiwuwar hakan. “Za mu duba wannan batu, domin babban nauyi ne,” inji shi.
Gwamnan ya ce, yawan ayyukan tattalin arziki da ake gudanarwa ba bisa ƙa’ida ba a Neja ya sa magance matsalar ke da wahala, yana mai cewa jihar ta mamaye kusan kashi 10 cikin 100 na faɗin ƙasar Nijeriya, sannan tana da ɗimbin albarkatun ma’adinai. “Haƙar ma’adinai, farautar dabbobin daji da sare itatuwa, duk manyan harkoki ne,” inji shi. “Jihar Neja ce ke da mafi yawan dazuzzuka da itatuwa a Yammacin Afirka, kuma mutane na can suna gudanar da sare itatuwa. Ba wai kawai tona ƙasa ba ne. Har da sare itatuwa, yin gawayi, kashe dabbobi da sayar da fatunsu da itatuwan, duk waɗannan abubuwa suna faruwa.”
Bago ya ce, haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba, farautar dabbobin daji da sare itatuwa na taimakawa wajen ƙara matsalar rashin tsaro a jihar, yana mai cewa wasu ’yan ƙasashen waje na da hannu wajen ɗaukar nauyin wacannan ayyuka da kuma gudanar da su. “Wasu ’yan ƙasashen waje suna cikin yankunanmu, suna gudanar da waɗannan ayyuka tare da ɗaukar nauyinsu, kuma ikonku yana da iyaka saboda akwai takura,” inji shi.
A cewarsa, hukumomin tsaro na sane da ayyukan, amma suna fuskantar takura saboda wasu daga cikin ’yan ƙasashen waje da ke gudanar da ayyukan suna da lasisi. “Sojoji sun san da hakan. DSS ta san da hakan. ’Yan sanda sun san da hakan. Amma an takaita musu hannu saboda waɗannan ’yan ƙasashen waje suna da lasisi,” inji shi.
“Don haka, ba batun gwamna ba ne. Ikon gwamna ya tsaya ne kan majalisarsa ta zartarwa. Gwamna dai ana kiransa babban jami’in tsaron jiha ne da baki kawai. Magana ce kawai; babu ikon da zai ba da umarni.”
