Wani tulu da aka yi imanin ya kai shekara 3,500 a duniya ya gamu da ajalinsa bayan wani ƙaramin yaro ya fasa shi a wani gidan ajiyar kayan tarihi da ke Isra’ila.
Gidan tarihin na Hecht Museum ya bayyana cewa an ƙera tulun ne tsakanin shekarun 2200 zuwa 1500 kafin haihuwar Annabi Isa – kuma ta musamman ne saboda ba abin da ya same shi.
A buɗe yake ba a cikin gilashi ba kuma a kusa da ƙofar shiga wurin.
Masu wurin sun ce tsautsayi ne kuma ma har an sake gayyatar yaron da iyayensa domin zagayawa da su cikin wurin.
“Akwai lokutan da ake lalata kayan tarihi da gangan, kuma mukan ɗauki tsattsauran mataki a kan hakan,” inji Lihi Laszlo da ke aiki da wurin ajiyar.
“A wannan karon, ba haka abin yake ba. An lalata tulun ne bisa kuskure kuma yaro ne ya yi hakan yayin ziyara. Saboda haka za mu ɗauki mataki ne daidai da hakan.”
