Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Mai Martaba Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, zai naɗa Arc. Ali Muktar Dambatta a matsayin Sa’in Kano, Hakimin Makoda a yau Juma’a a masallacin gidan Sarki da ke ƙofar Kudu.
Sanarwar naɗin ta fito ne a cikin wata wasiƙa mai ɗauke da sa hannun Matawallen Kano, Aliyu Ibrahim Ahmed da aka raba wa manema labarai a ranar 18 ga Oktoba, 2024.
Hakazalika wasiƙar naɗin ta umarci Ali Mukhtar da ya sanar da ‘yan uwa da abokan arziki domin su zo su taya sa murna a ranar.
Daga ƙarshe sai Masarautar Kano ta taya shi murna tare da fatan Allah alheri da addu’ar Allah Ya dafa masa.
A cikin waɗanda za a naɗa wa rawani yau ɗin, akwai ɗan Sarki Muhammadu Sanusi na farko, wato Aminu Muhammadu Sanusi matsayin Ciroman Kano.
Mahaifin Muhammad Sanusi II, Ambasada Aminu Sanusi ya taɓa riƙe sarautar, sannan Alhaji Nasiru Ado Bayero ya riƙe sarautar har zuwa lokacin da aka naɗa shi Sarkin Bichi a shekarar 2020.
Sauran waɗanda za a naɗa su ne Mahmud Aminu Yusufu a matsayin sabon Mai Unguwar Mundubawa; Dr. Abubakar Sanusi Usman Shehu II a matsayin ɗan Galadiman Kano da Alhaji Abubakar Aminu Sanusi (Wambai) a matsayin ɗan Madami.
Sauran su ne Sarki Yusuf Bayero a matsayin ‘Yan ɗaka da Abdullahi Idris Bayero a matsayin Fagacin Kano da Ado Abdullahi Aminu a matsayin Kaigaman Kano da Idris Sanusi a matsayin Sarkin Sulluɓawa da Mansur Isa Bayero a matsayin Sarkin Kudu sai Abdullahi Sarki Mohammed a matsayin Sarkin Yamma.
