Mahara sun kashe ’yan sanda huɗu a Katsina

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

’Yan bindiga sun kai hari wani sansanin ’yan sanda a Jihar Katsina, inda suka kashe jami’ai huɗu da wasu mutum biyu.

Sun kai harin ne sanssnin ’yan sandan kwantar da tarzoma da ke Garagi, a Karamar Hukumar Kankara.

Har wa yau, maharan sun yi awon gaba da bindigogin ’yan sanda.

Kazalika, sun kashe wasu mazauna garin guda biyu.

Wani mazaunin yankin da ya nemi a sakaya sunansa, ya ce maharan sun ƙone azuzuwan makarantar firamaren Tsamiyar Jino, inda jami’an tsaron suka kafa sansaninsu.

ƙoƙarin jin ta bakin kakakin rundunar ’yan sandan jihar, ASP Abubakar Sadiƙ Aliyu, ya ci tura zuwa lokacin haɗa wannan rahoto.

By ukarofi