Yin amaja ga masu aikin abincin buɗe-baki ya tunzura kwamishina a Jigawa 

Spread the love

Daga UMAR AKILU MAJERI a Dutse

Kwamashinan ayyuka na musamman, Alh Auwalu ɗanladi Sankara ya nuna damuwarsa kan yadda ake yi wa gwamnatin jihar zagon ƙasa ta fuskar ciyar da al’umma abinci a lokacin buɗe baki a mazaɓun da gwamnatin ta ware guda 634 albarkacin wata Ramadan.

Kamar yadda ya wallafa shafinsa na Facebook, Sankara ya ce “Mun samu labari da rahotanni na wasu cibiyoyi da ke samar da abincin shan ruwa (buɗa baki) da ba su cika ba a lokacin shirin ciyarwa na watan Ramadan da gwamnatin Jihar Jigawa ta shirya. A ƙasa akwai cibiyoyin da dillalan da suke kai abincin da bai cika ba.”

Ya yi misalai da ƙananan hukumomi kamar haka; A ƙaramar Hukumar Garki akwai;

Garki – B: an same su da rashin samar da isasshen abinci kamar yadda aka tsara a yi.

Sai ƙaramar Hukumar Gumel, a Gumel; Cibiya 1: Su ma an same su da rashin samar da isasshen abinci kamar yadda aka tsara a yi.

Haka zalika a ƙaramar Hukumar Guri, a ƙauyen Musari a akwati mai lamba 001: an same su da laifin rashin samar da isasshen abinci kamar yadda aka tsara.

Haka a ƙauyen – Adiyani a akwati mai lamba 001: Su ma an kama su da laifin rashin samar da isasshen abinci kamar yadda aka tsara bai wa jama’ar.

A akwati mai lamba ta 002, bincike ya nuna akwai rashin samar da isasshen abinci kamar yadda aka tsara a bai wa jama’a.

Kazalika, a ƙaramar hukumar Gwiwa a ƙauyen Shafe da Karshi: ƙunshin da bai cika ba ake rabawa jama’a.

Bugu da ƙari, a Gwiwa cikin gari da mazaɓar – Zauma da Sainawa: ƙunshin da bai cika ba aka rabawa jama’a saɓanin yadda aka tsaara.

A Haɗejia, a Unguwar Kasuwar Kudu (Cibiya A): Shinkafa da ƙosai 280 aka raba wa masu azumi.

Bayanai sun nuna cewa, a ƙaramar Hukumar Jahun a ƙauyen Kale (kale cikin gari): an samu rashin samar da isasshen abinci kamar yadda aka tsara.

Haka kuma a ƙauyen Bura-buri: Rashin samar da isasshen abinci kamar yadda aka tsara.

Binciken ya gano cewa, a Malam Madori a mazaɓar Arki, kunu kawai aka raba wa mutane da ƙosai 100.

A. Roni da Amaryawa (Cibiya A): shinkafa fakiti 107 kawai aka rabawa mutane.

Haka a Roni – Amaryawa (Cibiya A): ƙosai 170, shinkafa 100 dauri ɗari aka raba.

A ƙaramar hukumar ta Roni– Fara –Kagadama: Shinkafa da ledar kunu 208, kunu 207 aka rabawa mutane.

Kuma mazaɓar –Kwaita a Roni an samu rashin samar da isasshen abinci kamar yadda aka tsara.

A kwanan Huguma a ƙaramar humar Dutse, masallacin Malam Zakariyya Kandi da unguwar Zai Junction – Asabe Muhammad nan ma an samu ƙarancin abincin ba a yi shi kamar yadda aka ce a yi ba.

Kwanar Huguma a Dutse, Gida Dubu masallacin Malam Ismail Ringim–Ruƙayya M. Abdullahi.

Kwamashinan a cikin fushi ya ce, “a matsayina na Kwamishinan Ayyuka na Musamman da ke da alhakin kula da wannan shirin, ina so in yi gargaɗi ga duk wani dillali da masu ruwa da tsaki a wannan harkar na abincin ciyarwa na buɗa baki.”

Ya hori waɗanda gargaɗin ya shafa da su ɗauki gargaɗi ya zama sanarwa ta ƙarshe ga duk wanda ke da alhakin shirya abinci, duk wanda aka samu da bada ƙunshin da bai cika ba ko kuma aka same shi da hannu cikin kowane nau’i na rashin bin ƙa’ida ko amaja, to za a hukunta shi a ƙarƙashin doka.

By ukarofi