Yoyon fitsari: Gidauniya ta ceto rayuwar wasu mata a Gombe

Misis Rose Ajuji, wata mata mai shekaru 60 daga ƙaramar hukumar Billiri a Jihar Gombe, ta bayyana yadda ta kwashe shekaru 30 tana fama da ciwon yoyon fitsari, wanda ya sa mijinta ya guje ta.

Cikin kuka, Misis Rose ta bayyana cewa ta kamu da cutar ne lokacin da ta samu ciki wanda bai kammalu ba. Ta ce daga lokacin, mijinta da danginsa suka yi watsi da ita, har mijin ya mutu ba tare da sun sake haɗuwa ba. Tsawon wannan lokaci, ta ce tana fama da tsangwama daga al’umma, kuma ba ta sake aure ba.

Misis Rose ta yi godiya ga Gidauniyar Fistula Foundation Nigeria, wacce ta yi mata tiyata kyauta. Ta ce, “Sun ceto rayuwata a lokacin da na fidda tsammani. Ya kamata al’umma su gane cewa masu fama da wannan larura ba laifinsu bane, don haka bai kamata a nuna musu tsangwama ba.”

Ita ma wata matashiya, Rukayya Manir daga ƙaramar hukumar Tafawa Balewa a Jihar Bauchi, ta bayyana irin tsangwamar da ta sha saboda cutar yoyon fitsari. Ta ce, “Har ana ce min ‘mai zarnin fitsari’ idan na wuce mutane.”

Rukayya, wacce ta kamu da cutar bayan haihuwarta ta biyu, ta ce wannan shi ne karo na uku da ake mata tiyata, kuma tana fatan samun lafiya gaba ɗaya. Ta ƙara da cewa ta godewa gidauniyar Fistula Nigeria da ta taimaka mata.

Dakta Garba Muhammad Buwa, jami’in da ke jagorantar aikin tiyatar a asibitin ƙwararru na Gombe, ya bayyana cewa daga cikin mata 69 da suka zo neman jinya, guda 50 kawai aka tantance cewa suna da ciwon yoyon fitsari.

A cewarsa, “Wasu daga cikin su an riga an yi musu tiyata har sau bakwai kafin wannan karon. Wannan matsala na bukatar kulawa ta musamman domin rage dawowa asibiti.”

Ya kuma bayyana cewa mafi yawan cutar na faruwa ne sakamakon rashin kula da kyau lokacin haihuwa, musamman idan mace ta yi doguwar naƙuda ko aka yi kuskuren magani.

Shugaban gidauniyar, Musa Isa (Baba Musa), ya ce suna gudanar da ayyukan tiyata kyauta a jihohi daban-daban na Nijeriya. A watan Maris 2024, sun gudanar da aikin gangami a Gombe, inda suka yi wa mata da dama tiyata.

Baba Musa ya ce, “A Jihar Kano kawai, fiye da rabin matan da ake yiwa tiyata sabbin kamuwa ne. Wannan ya nuna cewa cutar na ƙaruwa, sai an dage wajen wayar da kai da ɗaukar matakan gaggawa.”

A shekarar 2024, gidauniyar ta horar da mata 50 da aka yiwa tiyata kan sana’o’in dogaro da kai tare da ba su aikin zaƙulo masu fama da cutar a karkara domin kawo su neman magani.

Gidauniyar ta yi kira ga gwamnatocin jihohi da su horas da likitoci da ma’aikatan jinya domin inganta kula da mata masu ciki. Haka kuma, sun nemi al’umma da su guji barin mata masu juna biyu cikin doguwar nakuda a gida, wanda shi ne babbar hanyar kamuwa da cutar.