Zaɓen 2023: Gawuna da Abba a mahanga uku

Daga FATUHU MUSTAFA

A yanzu dai saura ‘yan watanni suka rage a yi zaɓen shugaban ƙasa. Wanda zai zo a watan Fabrairu na shekarar baɗi. Tuni dai jam’iyya mai ci a Jihar Kano wato APC, ta tsayar da dan takararta, wato Mataimakin Gwamnan Kano, Nasiru Yusuf Gawuna. Inda kuma ake kyautata zaton babbar jam’iyyar adawa ta NNPP mai kayan daɗi za ta ƙara tsai da zakaran gwajin dafinta, wato Abba Kabir Yusuf da aka fi sani da Abba Gida Gida. A wannan nazari da na yi, ina son na kalli ƙalubalen dake gaban ɗan takarar jam’iyya mai ci, wato Nasiru Gawuna, musamman idan aka yi la’akari da abokin karawar sa, Abba Gida-gida. 

Mahanga ta farko: Mahangar masu zaɓe:
A ganina, za a iya kasa masu zaɓe a Kano, wanda za su yi tasiri gida biyu: Matasa da mata a ɓangaren ɗaya, sannan manya. Kashi 70 na masu zaɓe a Kano matasa ne, waɗanda Gwamnatin Ganduje ta yi watsi da su a tsawon shekaru 8 da ta shafe tana mulki. Kodayake an bai wa wasu matasa muƙamai har ma da na Kwamishinoni. Amma gwamnatin ba ta zo da wani tsari da matasan da basu da muƙami za su amfana ba, walau dai ta hanyar samar da ayyukan yi ko kuma samar da guraben karatu kamar yadda gwamnatin da ta gabata ta yi ba. Da yawa matasan nan ɗore suka yi. Wanda hakan ya sa, suka fito ƙwansu da kwarkwatarsu a zaɓen 2019, don ganin sun kayar da gwannati mai ci a yanzu. Babban burinsu shi ne, su dawo da gwamnatin Kwankwasiyya wacce ta ba su guraben karatu har a kasashen waje. Sannan ta kuma ƙirƙiro musu hanyoyin samun kuɗaɗe da ayyukan yi. Akwai babban ƙalubale a gaban Gawuna ya nemi yadda zai yi ya shawo kan waɗannan matasa su amince ba za a je yaƙi da su, idan an ci nasara a zo rabo a ba su kuturun bawa ba. 

A dai ɓangaren masu zaɓen, akwai kashi 30 da ya rage na masu zaɓe, waɗannan ma fi akasarinsu, ma’aikata ne da ‘yan fansho. Kusan a iya cewa, ba waɗanda suka sha azaba a hannun wannan gwamnatin irin yan albashi da ‘yan fansho. Saboda yadda gwamnatin ta ringa yanke musu albashi ba kai ba gindi da sunan haraji. Wannan ɓangare na masu jefa ƙuri’a kusan a shirye suke da su dau matakin ganin bayan wannan gwamnati a shekara mai zuwa. Domin sun gaji da tsarin nan na, kura da shan bugu, gardi da ƙwace kuɗi. 

Ɓangare na uku da su ma suna nan sun wasa wuƙarsu da nufin su ga sun ga bayan wannan gwamnati su ne, mabiya aƙidun addini, musamman ‘yan Tijjaniya magoya bayan Halifa Muhammadu Sunusi II. Da kuma magoya bayan Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara, da suke kallon an haɗa kai da gwamnati an yi wa malamin su sharri. Gawuna na da jan aiki wurin ganin ya tabbatar wa da waɗannan cewa, gwamnatinsa ba irin ta maigidansa ba ce. 

Mahanga ta biyu: Shiyyar sanatoci uku:
Bari mu kalli sanatoci uku da ake da su a Kano. Sanatoriya ta tsakiya dai, ita ke da sama da kashi 50 na yawan ƙuri’u a Kano. Kuma kowa ya san gida biyu ke juya ta, gidan Malam Ibrahim Shekarau da kuma gidan Kwankwaso.

Dama ba a maganar Kwankwaso, domin kowa ya san matsayarsa. To amma a dambarwar da ake ciki a yanzu, tunda Shekarau ya bar jam’iyyar APC zuwa NNPP, to ko shakka babu, ba maganar APC a Sanatoriya ta tsakiya. Tunda a kan hanyarsa ta neman makoma ya yada zango kasuwar ‘Yanlemo dake Miller Road ya kwashi kayan daɗi. Ko shakka babu, Gawuna na da babban ƙalubale a gabansa, domin ba yadda za a yi a kayar da waɗannan biyun a Sanatoriya ta tsakiya. 

A ɗauki sanatoriya ta Kudu da ta haɗa da Rano, Garun Malam, Bunkure, Bebeji, Kiru, Wudil, Gaya, Sumaila, Ajingi da Dawakin Kudu da Rano. A wannan ɓangare ban ga mai ƙarfin Tsohon Kakaki  kuma dan Majalisar Tarayya Alasan Rurum turakin Rano ba. Musamman a Rano, Bunkure da Garun Malam ba. Barin sa jam’iyyar APC ba ƙaramin naƙasu ba ne ga jam’iyyar a zaɓe mai zuwa. Ya zama wajibi Gawuna ya samo wani zaƙaƙurin da zai maye masa gurbin Turakin Rano. Daɗin daɗawa kuma ga Kawu Sumaila da shi ma ya fice daga jam’iyyar. Wanda hakan ke nuni da cewa, ita ma Sumaila za a iya rasa ta. 

Ba inda za a yi zube ban ƙwaryata irin Sanatoriya ta Arewa. Domin dukkan mataimakan gwamnan daga nan suka fito. In har NNPP ta tsayar da Aminu Abdussalam a matsayin mataimaki. Wani ƙarin ƙalubalen shi ne, ficewar Sanata Barau Jibrin Maliya daga APC. Matuƙar wannan ficewa ta tabbata, to ko shakka babu, za a rasa dukkan ƙananan hukumomi da dama a wannan yanki. Lallai ayi hattara!! 

Mahanga ta uku: Sabbin masarautu 
Idan har da abinda zai ƙara zamar wa Gawuna matsala a lokacin kamfen din sa, ina ganin sabbin masarautu na ciki. Da farko dai, ba kowacce ƙaramar Hukuma ce ke marhabin da wannan sauyi ba. Wasu na ganin, yin sabbin masarautun bai da wani tasiri a cigaban ƙananan Hukumominsu.

Wasu na tambayar ta yaya, yin masarauta a Bichi ya amfani ƙaramar Hukumar Tsanyawa, ko ta Ƙunci? Wanda ke Dambatta na kallon an ƙasƙantar da ƙaramar hukumarsa, domin ya shi da yake Kano,  ya zai koma ƙarƙashin masarautar Bichi? 

Da yawa daga ‘ya’yan gidan sarauta, wato Gidan Dabo na kallon cewa, an ci musu fuska, domin an sanya sun koma ƙarƙashin hakimansu na da, sun zama barori a masarautarsu. Waɗannan kaɗan ne daga irin ƙorafe-ƙorafen da suka biyo bayan kafa sabbin masarautun. Kar kuma a manta, akwai ‘yan majalisu 4 da a yau aka ƙwace musu garuruwan su na gado, wato Sarkin Bai (Dambatta), Madaki (Dawakin Tofa), Sarkin Dawaki Maituta (Gabasawa) da kuma Makama (Wudil). Waɗannan manyan hakimai a yau ba ɗaya da aka bar masa gari, sun zama su da jeka-nayi-ka duk ɗaya. Su kansu har yanzu suna nan, suna dakon yadda za su dawo kan ikon su na da, kamar yadda ya ke a tsarin sarautar gargajiya. 

Yanzu dai shawara ta rage ta mai shiga rijiya; dole Gawuna ya san yadda zai tsara yaƙin neman zavensa, idan kuwa ba haka ba, zai ji kiɗa a Magwan. Allah ya sa mu ga alheri! 

Fatihu marubuci ne, ya rubuto ne daga Abuja