Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Jam’iyyar ADC ta bayyana wani sabon tsarin raba madafun iko da nufin haɗa kan ‘yan jam’iyyun adawa gabanin zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 2027, a daidai lokacin da ake fargabar cewa rikicin neman tikiti na iya haddasa saɓani bayan an kammala zaɓen fidda gwani.
Da ya ke magana kan lamarin a shirin The Morning Show na gidan talabijin na Arise Tɓ a ranar Litinin, Lukman Salihu, ɗaya daga cikin manyan jiga-jigan jam’iyyar kuma mai inganta sauye-sauyen ta, ya ce tsarin an kirkiro shi ne domin ƙarfafa jam’iyyar da kuma rage taruwar iko a hannun mutum guda.
Wannan mataki na zuwa ne yayin da fafatawa ke ƙara zafi a cikin ‘yan adawa, inda magoya bayan Peter Obi, Rabiu Musa Kwankwaso, Atiku Abubakar da Rotimi Amaechi ke gabatar da mabanbantan ra’ayoyi kan wanda ya kamata ya jagoranci hadakar.
Sai dai Salihu ya ce kada a dauki wannan sabani a matsayin rarrabuwar kai.
A cewarsa, manufar ita ce tabbatar da cewa duk masu neman takara suna da ruwa a cikin tsarin, ko da wanene ya fito a karshe.
Baya ga tsarin raba iko, jam’iyyar ta ce ta kammala tsara manufofin gudanar da mulki, wadanda suka dogara da kundin tsarin manufofi da aka amince da shi a babban taron ta na karshe.
Ya ce rikice-rikicen shari’a da matsalolin cikin gida ne suka jinkirta bayyana jadawalin tsare-tsaren a fili, amma ya nuna kwarin gwiwa cewa za a kammala aikin nan ba da jimawa ba.
Salihu ya kuma soki jam’iyya mai mulki ta APC, yana mai cewa ta kauce daga manufofin da aka kafa ta a kai.
