Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Shugaban kwamitin sauraren ƙorafe ƙorafe na jam’iyar APC a zaɓen gundumomin ƙananan hukumomin jihar da ya gudana Malam Jamilu Uwais Zaki ya faɗawa manema labarai haka, wanda ya ce gudanar da zaɓen ba tare da ƙorafi ba na nuna alamun nasarar jam’iyar a zaɓen 2027.
Uwais ya bayyana cewa sakamakon zaɓen shugabannin jam’iyar a waɗannan matakai ya nuna gaskiya da adalci da kuma ba duk wani ɗan jami’ya damar ayi da shi.
Ya yaba wa ‘yan takarar kan yadda suka nuna halin manyantaka wajen gudanar da zaɓen cikin kwanciyar hankali.
Shugaban kwamitin ya bayyana cewa kwatanta gaskiya da adalci a zaɓen yan jam’iyar da ya gudana a jihar ta tabbatar da jajircewar jam’iyar APC wajen yiwa kowa adalci.
“Yi wa kowa adalci a gudanar da zaɓen ya’yan jam’iyar ta tabbatar da akwai ɗa’a da dimokraɗiyya a cikin jam’iyar APC.
Uwais ya ce an kammala zaɓen ba tare da ƙorafi ko koke ba, wanda kuma ya gudana ne ta sasanci tsakanin ‘yan takara.
An nasa ɓangaren kuwa shugaban kwamitin tantance ‘yan takara Bashir Ibrahim Boni ya ce a gudanar da tantance ‘yan kakarar ba tare da wata matsala ba.
Ya ce sai da yan takarar suka tabbatar da su ya’yan jam’iyar APC ne tare da miƙa duk takardar da kwamitin ta bukata kafin gudanar da zaɓe.
Ibrahim Boni ya yaba wa kwamitin shirya taron da yace sun taimaka wajen samun nasarar tantancewar.
A nasa jawabin shugaban kwamitin shirya taron wanda har ila yau shugaban ma’aikatan gidan gwamnatin Katsina Hon Abdukadir Nasir Andaje ya bayyana cewa an gudanar da zaɓen shugabannin a unguwanni 361 da ke faɗin jihar.
Andaje ya bayyana cewa an bi dokoki da ƙa’idoji da jam’iyar ta tanada wajen gudanar da zaɓen.
