Daga MUHAMMADU MUJJITABA a Kano
An bayyana cewa yadda zaɓen ƙungiyar ɗalibai ta ƙasa NAKSS reshen Jihar Kano cikin kwanciyar hankali da lumana abun farin ciki ne, kuma nasara ne ga ɗaliban Jihar kano da na Nijeriya baki ɗaya, kamar dai yadda mai ba gwamnan Kano Shawara kan Harkokin Ɗalibai Hon Ibrahim Ma’aji ya bayana bayan kammala zaɓen da kuma rantsar da shugabanin NAKSS a ranar Lahadi da ta gabata.
Sai kuma yadda ɗaliban Kano da ke karatu a manyan makarantun kano da sasan ƙasar nan yanzu haka sun zaɓi kwamred Isyaku Ali Kanwa, a matsayin sabon shugaban ƙungiyar ɗalibai ta ƙasa reshen Jihar Kano da aka fi sani da NAKSS wato NATIONAL ASSOCIATION OF KANO STATE STUDENTS a matsayin shugaba da zai shekara guda yana jan ragamar ƙungiyar kamar yadda ya ke a kundin tsarin mulkin NAKSS kuma ya samu ƙuri’a 83, inda ya ci ba hamayya.
Sauran shugabanin da aka zaɓa su ne; Rabiu Muhammad Sa’ad, mataimakin shugaba na ɗaya, Sabiu Rabiu Kabo, babban sakatare, Zainab Musa Ismail, mataimakiya ta biyu, Muhammad Ghali Muhammad, Mataimakinsa, Abdulyasar Muhammad Dabo, Ma’aji Mustapha Abdu Saye, mai kula da walwalar ɗalibai Abdulkarim Idris Namadi, sakataren kuɗi Maryam Bala Isah, mai kula da walwala ta biyu, Fiddausi Abdulkarim Salihu, jami’ar wayer da kan ɗalibai, Abubakar Abdullahi, Jami’in kula da zamantakewa, Abdullahi Ali Gambo, mai binciken kuɗi, Ahmad Kamisu Umar, jami’in kula da wasanni na ɗaya, sai kuma Mustapha Mustapha Bashir, Jami’in yaɗa labarai na ɗaya, Shehu Aminu Jami’in yaɗa labarai na biyu.
Shi dai wannan zaɓe an yi shi ne a Asabar ɗin nan da ta gabata bisa tsatsauran tsaro wanda ya haɗa jami’an ’yan sanda na Sibil Difens da jami’an tsaro na farin kaya daban daban, Karota, kuma an yi zaɓen ne ƙarƙashin sanya idon Hon Ibrahim Ma’aji Sumaila, mai ba Gwamnan Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf, Shawara kan harkokin ɗaliban Jihar Kano, inda kuma ya bayana gamsuwa da yadda zaɓen ya kasance cikin lafiya da kwanciyar hankali.
Shugaban ƙungiyar Isyaku Ali Kanwa, ya yi alƙawarin kyautata rayuwar ɗalibain Jihar Kano, ta hanyar samun haɗin kan gwamnatin Kano da sauran masu ruwa da tsaki a harkar ɗalibai kwamred Usman Maidala, shi ne shugaban da ya jagoranci gabatar da wannan zaɓe da mataimakinsa Abdulganiyu Ɗalhatu, wajen gabatar da zaɓen ƙungiyar ɗalibai ta NAKSS Kano.
