Za a ɗaure ɗan wasan Jamus, Jerome Boateng da laifin dukan budurwarsa

Spread the love

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Kotu a Jamus ta tabbatar da laifin cin zarafi kan fitaccen ɗan wasan ƙwallon ƙafar ƙasar Jerome Boateng, wanda ake tuhuma da laifin dukan tsohuwar budurwarsa a shekarar 2018.

A shekarar da ta gabata ne kotu ta samu Boateng da laifin cin zarafin tsohuwar abokiyar zamansa, mahaifiyar ’ya’yansa tagwaye mata, a lokacin hutun Caribbean shekaru huɗu da suka wuce, makwanni bayan kammala gasar cin kofin duniya a Rasha.

Sai dai kotun da ke gundumar Munich ta rage yawan tarar da a baya aka buƙaci Jerome Boateng ya biya daga Yuro miliyan 1.8 zuwa Yuro miliyan 1.2.

Ɗan wasan dai ya sha musanta zarge-zargen da ake yi masa tare da ɗaukaka ƙarar neman wanke shi daga tuhumar.

Yayin zaman farko na shari’ar da aka musu, tsohuwar Sahibar Boateng ta shaidawa kotun cewa ɗan wasan ya zafga mata naushin da saboda ƙarfinta, wanda hakan ya sa ta rasa numfashi na ɗan wani lokaci yayin wata zazzafar cacar baki da ta kaure tsakaninsu.

By Editor