An samu tashin gobara a wani sashen ginin hukumar NYSC a Abuja

Daga BASHIR ISAH

Rahotanni sun nuna cewa, gobara ta ci wani sashe na ginin Babban Ofishin Kula da Harkokin ‘Yan yi wa Ƙasa Hidima (NYSC) da ke Abuja.

Bayanai sun ce iftila’in ya auku ne da safen ranar Juma’a.

Daraktan yada labarai na ma’aikatar, Eddy Megwa ya tabbatar da faruwar lamarin.

Ya ƙara da cewa, gobarar ta faru ne a hawa na uku na ginin benen mai hawa shida.

Ya ce ba a samu asarar rai ba yayin gobarar, kuma wasu kayan aiki ne gobarar ta shafa.