Gwamnatin Buhari ta yi buris da batun komawar ASUU sabon yajin aiki

Daga AMINA YUSUF ALI

Gwamnatin Buhari ta ja bakinta ta yi gum, bayan da ƙungiyar Malaman jami’o’i ta ASUU ta sake tsunduma wani sabon yajin aiki.

Rahotanni sun bayyana cewa, ASUUn ta shiga wannan sabon yajin aikin ne sakamakon biyan ‘ya’yan ƙungiyar rabin albashi a watan Oktoba da Gwamnatin Tarayyar ta yi.

Wasu rahotannin sun sake bayyana cewa, gwamnatin ta biya ma’aikatan kuɗin kwanaki 18 kacal ne kawai da suka yi aiki a watan Oktoba.

Idan za a iya tunawa, a ranar Juma’a 16 ga watan Oktoban 2022 ne dai ASUU ta janye dogon yajin aikin da ta tafi na tsahon watanni 8.

Inda aka rufe dukkan makarantun jami’o’i mallakar gwamnati da suke a faɗin ƙasar nan. Yajin aikin nasu yana da nasaba da rashin cika wasu alƙawurra da gwamnatin ta ɗaukar musu tsahon shekaru.

A yayin da ake cikin yajin aikin ne dai, Ministan Ilimin Malam Adamu Adamu ya yi ikirarin cewa, gwamnati ta cika alƙawurran daga ɓangarenta.

Wanda a cewar sa, gwamnatin ta ba wa ƙungiyar ASUU Naira biliyan 50 da za ta biya haƙƙoƙin ma’aikata masu koyarwa da marasa koyarwa a jami’o’in.

Kodayake, ASUU a lokacin ta ƙi komawa aiki saboda dagewar gwamnatin a kan ba za ta biya su albashinsu na watannin da suka kasance a yajin aiki ba. Amma duk da haka, ba su koma aiki ba.

Ana haka ne kuma, gwamnatin ta gurfanar da ASUU a gaban kuliya, inda ta nemi kotun ta ba da odar da za ta tilasta wa mambobin na ASUU komawa bakin aiki.

Kotun masana’antun ta zartar da hukunci a kan lallai ma’aikatan su koma bakin aiki.

A yayin zantawarsa da ‘yan jaridu, wani jigo daga cikin majalisar zartarwar ƙungiyar ya koka da yadda gwamnatin ta tunzura mambobinsu ta hanyar biyan su rabin albashi.

Inda mambobin nasu suke zargin su masu zartarwar ƙungiyar a kan halin da suka samu kansu.

Wani kuma mamban ƙungiyar ya bayyana cewa, bisa dukkan alamomi wannan gwamnatin ta dage sai ta ga bayan ƙungiyoyi a ƙasar nan.

A cewar sa, ya samu labarin cewa, Ministan Ƙwadago da Ayyuka, Ngige, shi ya aike wa da babban akanta janar takarda ya umarce su da su biya ma’aikatan albashin iyakacin lokacin da suka dawo daga yajin aiki. Amma sam ba ma a tuntuɓe su ba.

Kodayake dai, har yau gwamnatin Tarayyar ba ta tofa ta bakinta ba a kan dalilinta na biyan rabin albashi ba, amma dai bisa dukkan alamu ta yanke hukuncin biyan rabin albashi ne saboda ASUU sun koma bakin aiki bayan sun ci rabin watan na Oktoba.

A yayin da aka tuntubi Malam Adamu, Ministan ilimi a game da batun, sai mai magana da yawun ma’aikatar ilimin ta tarayya ya kada baki ya ce, “Mu ba ma biyan albashi a ma’aikatar ilimi.

“Ku daure ku miƙa ƙorafinku i zuwa ofishin akanta janar,” inji shi.