Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Ministar Kuɗi, Kasafi da Tsare-tsare, Zainab Shamsuna Ahmed, ta tabbatar da cewa shirin Babban Bankin Nijeriya (CBN) na sauya fasalin Naira yana da matuƙar haɗari ga tattalin arzikin ƙasar nan.
Zainab, wacce ta bayyana haka a gaban kwamitin kuɗaɗe na Majalisar Dattawa a lokacin da take kare kasafin kuɗin ma’aikatar ta ranar Juma’a, ta jaddada cewa, shirin na CBN na sauya wasu takardun kuɗi, zai ƙara karya darajar Naira.
“Masu girma sanatoci, CBN bai tuntuɓe mu a Ma’aikatar Kuɗi ba kafin ɗaukar wannan mataki na sauya wasu takardun Naira ba, don haka ba za mu iya aron bakinsu mu ci musu albasa ba.
“Amma a matsayina na babbar jami’a a harkar tsare-tsaren kuɗi a Nijeriya, wannan tsarin da ake shirin aiwatarwa a yanzu, ya na da matuƙar haɗari ga darajar Naira a kasuwar canjin kuɗaɗe.”
Bayanin nata na zuwa ne bayan Sanata Michael Okpeyemi Bamidele, ya yi mata ƙorafi cewa kwana biyu kacal bayan CBN ya sanar da shirin sauya takardun Naira 100 zuwa 1,000, amma farashin canjin Dala ya yi tashin gwauron zabo daga Naira 740 zuwa Naira 788.
A ranar Laraba ne Gwmanan CBN, Godwin Emefiele ya sanar da sauya takardun kuɗin daga ranar 15 ga watan Disamba, 2022.
