Za a nuna liyafar murnar bikin Yuanxiao ta talibijin yau

Daga CRI HAUSA

Yau 15 ga watan Janairu bisa kalandar gargajiyar ƙasar Sin, rana ce ta bikin Yuanxiao, inda a kan kunna fitilu masu siffofi daban-daban tare da cin wani nau’in abinci mai suna Yuanxiao don murnar bikin.

Ban da wannan kuma, za a nuna wata liyafar waƙe-waƙe da raye-raye yau ta talibijin da babban gidan rediyo da talibijin na ƙasar Sin na CMG ya tsara, inda za a mai da hankali kan batutuwan da ke shafar gasar wasannin Olympics na lokacin sanyi ta Beijing, sha’anin binciken samarin samaniya na Sin, da ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta mata ta Sin da dai sauransu.

Sa’an nan liyafar za ta haɗa kimiyya da fasaha da fasahar wasanni tare, a ƙoƙarin samar wa masu kallo wata kyakkyawar liyafa mai cike da zamani da al’adu da kimiyya da fasaha.