Za a shirya fim akan tarihin Nana Asma’u, ɗiyar Shehu Usman Ɗan Fodiyo

Spread the love

Mai alfarma Sarkin Musulmi, Muhammadu Sa’adu Abubakar na III tare da Ma’aikatar Masana’antu, Kasuwanci da Zuba Jari ta Nijeriya sun amince wa wani kamfani ya fara aikin shirya fim kan rayuwa da bajintar Nana Asma’u, wadda fitacciyar malama, mawallafiya kuma mai fafutukar ilimi ce a ƙarni na 19.

Fim ɗin zai nuna irin gudummawar da Nana Asma’u, diyar Shehu Usman Ɗan Fodiyo, ta bayar wajen ilmantarwa, karfafa mata da gina ilimin addini, tare da ba da gudummawa ga zaman lafiya da fahimtar juna tsakanin al’ummomin Nijeriya.

Da take ƙarin haske kan aikin, Mai ƙoƙarin shirya fim din Hajiya Rahma Abdulmajid ta ce rayuwar Nana Asma’u hujja ce ta tarihi cewa ilimin mata tushensa yana cikin al’adar Arewa da addinin Musulunci, ba wani sabon abu daga waje ba.

“….labarin fim din zai farfado da ilmin ‘ya’ya mata a Arewacin Nijeriya, hada kai da kawo zaman lafiya a kasa”, inji ta.

Ta kuma nuna irin ilimin da Nana Asma’u ta yada zai taimaka wajen karya tunanin cewa karatun mata sabuwar al’ada ce da ba ta dace da yankin Arewa ba. Ta kara da cewa, rashin ilimi na haifar da rauni a zamantakewa, rashin bin addini yadda ya kamata, tsattsauran ra’ayi da kuma amfani da mata wajen siyasa ta hanyar da ba ta dace ba.

By Babaji