
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Ƙungiyar masu Shirya fina-finai ta ƙasa (MOPPAN) ƙarƙashin jagorancin Shehu Hassan Kano, ta fitar da saƙonta na taya murna ga Elder El-Sa’eed Yakubu Lere bisa samun muƙami a gwamnatin Jihar Kaduna.
MOPPAN, a wata takardar daga Sakatarenta na ƙasa, Dakta Muhammad Ibrahim Gumel, ta ce shugaban ƙungiyar, jagororinta a matakin ƙasa da na jihohi da ɗaukacin ƴan masana’antar Kannywood suna taya El-Sa’eed murna.
Haka kuma, suna miƙa jinjinarsu ga Gwamnan jihar, Uba Sani bisa ba El-Sa’eed muƙamin na Shugaban Hukumar Kula da Lamuran Yaɗa Labarai na jihar (KSMC).
A ƙarshe, MOPPAN ta yi masa addu’ar fatan Allah ta taya shi riƙe muƙamin bisa gaskiya da adalci tare da kammalawa cikin nasara.
