Musa Iliyasu Kwankwaso: Shekaru 60 masu albarka

Spread the love

Daga SHEHU MUSTAPHA CHAJI

Allah ya albarkaci Jihar Kano da mutane da suka shahara suka ɗaukaka a fannoni daban daban na rayuwa, suke kuma bada gudunmawar su domin cigaban al’umma. Hon. (Dr) Musa Iliyasu Kwankwaso yana cikin jerin kanawa da suka sami ɗaukaka da shahara a fannonin da suka zabar wa kansu dan bada gudunmawar su dan cigaban Jihar Kano da Arewa da Najeriya.
Tarihin dimokuraɗiyyar mu ba zai taɓa cika ba sai an nakalto tarihin gwagwarmaya da gudunmawar Musa Iliyasu Kwankwaso.
Ya kasance cikin mutanen da suka sa siyasar Kano ta zama ta daman saboda suna ƙoƙarin ganin cewa al’umma na kwasar romon dimokuraɗiyya da samun ayyukan cigaban ƙasa. Ya kuma kwashi shekaru yana sharhi kan harkokin siyasa da lissafin siyasa har hakan yasa wasu ke kiran sa likitan siyasar Jihar Kano.
Musa Iliyasu Kwankwaso ɗan Siyasa ne na kusa da al’umma kuma ya kasance cikin alamomin dimokuraɗiyya da samar da shugabanci na gari a Jihar Kano da wajen jihar.

Musa Iliyasu Kwankwaso ya kwashi tsawon shekaru yana hidima ga al’umma. Yayi aiki a Ma’aikatar Ruwa na Jihar Kano har ya kai matsayin muƙaddashin darakta. Ya zama shugaban ƙaramar hukumar Madobi har karo biyu. Ya kuma zama mutumin da ya fi dadewa yana riƙe da muƙamin kwamishina a Jihar Kano. Malam Ibrahim Shekarau ya naɗa shi kwamishinan ayyuka na musamman daga bisa ni ya canza shi zuwa ma’aikatar raya karkara da cigaban al’umma. Shima Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya sake naɗa shi a matsayin kwamishinan ma’aikatar raya karkara da cigaban al’umma a karo na biyu.

Musa Iliyasu Kwankwaso ya bar tarihin ayyukan cigaban ƙasa da kawo cigaba a muƙaman da ya riƙe. Ya kasance mutumin da a kullum ƙoƙarin sa ya gan al’ummar sa sun sami cigaba. Ya kan kuma fifita buƙatun al’ummar sa kan nasa.
Hon. Musa Iliyasu Kwankwaso na daban ne cikin yan siyasa saboda hidima da taimakon al’umma. Shine ɗan siyasar da zai baka ba tare da ka tambaya ba. Sannan yana da ƙoƙarin sada zumunci da ziyarce ziyarce dan taya murna ko ta’aziyya ko jaje ga yan’uwa da abokai da magoya baya da abokan hulɗa. Kullum ƙoƙarin sa samar da cigaba da taimakon al’umma.
Kuma salon siyasar Musa Iliyasu Kwankwaso baya siyasa da gaba ko cin mutunci ko tada zaune tsaye. A salon siyasar sa kasancewar yana kusa da na ƙasa a kullum yana zaƙulo masu yiwa Jam’iyyar APC hidima yana taimaka musu dan su sami ƙwarin gwiwar ana sane da ƙoƙarin su. Ya kuma faɗaɗa wannan ƙoƙarin nasa wajen taimakawa masu yaɗa manufofin shugaba Bola Ahmed Tinubu a Jihar Kano.
Musa Iliyasu Kwankwaso jarumi ne mara tsoro a ƙoƙarin sa na ganin an samar da shugabanci na gari da al’umma su mori romon dimokuraɗiyya a Jihar Kano.

Ya kuma kasance cikin yan ƙalilan da suke goyon bayan Shugaba Tinubu saboda fahimtar kyakyawan manufar sa na ɗora Najeriya a tafarkin cigaba da bunƙasar tattalin arziki. Ya kasance cikin masu da’awar tunatar da yan Arewa ayyukan cigaba da Shugaba Tinubu keyi a Jihar Kano da Arewacin Najeriya.
Sarkin Yaƙin Karaye Mai Murabus ya kasance cikin mutanen da Shugaba Tinubu ya naɗa su jagoranci hukumar kogunan Hadejia da Jama’are. Shugaba Tinubu ya naɗa Hon. Musa Iliyasu Kwankwaso a matsayin babban daraktan kuɗi na hukumar.

Gogewa da sanin aikin Musa Iliyasu Kwankwaso ya taimaka ƙwarai wajen ayyukan cigaba da Engr. Rabiu Suleiman Bichi ke yi a hukumar kogunan Hadejia da Jama’are. Masha Allah, a wannan shekarar ba’a sami ambaliya a Jihohin Kano da Jigawa da Bauchi ba. Kuma hukumar hadejia da Jama’are ta zama ta daya a ma’aikatun gwamnatin tarraya da suke Jihar Kano da suka fi biyan haraji ga hukumar haraji ta ƙasa a wannan shekarar 2025.
Hon.(Dr) Musa Iliyasu Kwankwaso ya kafa tarihi wajen bunkasar Jihar Kano a fannonin samar da ayyukan cigaban ƙasa da bunƙasa da ɗorewar dimokuraɗiyya. Yan gwagwarmayar dimokuraɗiyya da samar da shugabanci na gari za su cigaba da tallata gwaraza irin sa domin ya zama abin koyi musamman ga matasan mu.
Muna fatan Allah ya ƙarawa Musa Iliyasu Kwankwaso lafiya da tsawon shekaru da ƙarin ɗaukaka da bunƙasar tattalin arziki domin ya cigaba da taimakon al’umma. Muna yi masa fatan Allah ya ƙara masa matsayi da manyan muƙamai.

Amb. Shehu Mustapha Chaji

By ukarofi