Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano
Shugaban haɗaɗɗiyar ƙungiyar ma’aikatan lafiya na jihar Kano, Kwamared Babangida Musa ya bayyana mutuƙar farin cikinsa game da matakin da Gwamnan Jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf yake ɗauka na biyan ‘yan fansho haƙƙoƙinsu wanda a baya aka daɗe ba a biya.
Ya ce su shaida ne a baya yadda ake ta gwagwarmayar a biya ‘yan fanshon har ana fitowa zanga-zanga da har wasu su faɗi su mutu amma yau gashi cikin murna da farin ciki mutane da suka gama aiki suka ɗauki dogon lokaci suka yi ritaya ana biyansu ba tare da tayar da jijiyar wuya ba.
Ya ƙara da cewa babu abinda za su cewa Gwamna Abba Kabir sai dai Allah ya saka da alkhairi ya yi riƙo da hannayensa kullum abinda ya shafi haƙƙin talakawa da ma’aikata yana iya bakin ƙoƙari domin sauke nauyin da Allah ya ɗora masa.
Ya yi nuni da cewa kwanan nan Gwamna ya biya ma’aikata mafi ƙarancin albashi na N71,000 wanda jihohin da suke Arewa maso yamma basu biya ba.Don haka ya ja hankalin ma’aikata su tsaya su riƙe aikinsu da kyau domin su tallafawa wannan gwamnati domin tana sauke nauyinta.
Shugaban haɗaɗɗiyar ƙungiyar ma’aikatan lafiyar na jihar Kano ya ce su ma za so su bar manufa mai kyakkyawa a wannan ƙungiya da yake shugabanta kamar yanda Gwamnatin Abba Kabir Yusuf yake jajircewa haka suma suke su jajirce su tallafawa manufar gwamnatin Kano akan inganta lafiya.
Kwamared Babangida Musa shugaban haɗaɗɗiyar ƙungiyar ma’aikatan lafiya na jihar Kano ya ce a baya ana samun yin sakaci da aiki sakamakon yanda Gwamnati data gaba ta bata bada kulawa ga ma’aikatan amma zuwan wannan Gwamnati a tsaye take akan kula da haƙƙoƙinsu su kuma a ƙungiyan ce za su tsaya su tabbatar ma’aikata sun yi abinda ya kamata domin ci gaban harkar lafiya a jihar Kano.