Ma’aikacin EFCC ya tsere bayan ya sace sama da dala 30,000 a ofis 

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja 

Wani jami’in da ke kula da ɗakin ajiye kayan laifi na hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa, EFCC, a ofishin shiyyar Kaduna ya tsere da sama da dala 30,000 da wasu kayayyaki masu daraja.

A tuna cewa tun a farkon watan Janairu, EFCC ta ce ta tsare jami’anta 10 a Legas bisa satar wasu kayan aiki da ba a iya tantance adadinsu ba, inda binciken Daily Nigerian ya gano cewa gwala-gwalai ne da kuɗaɗen ƙasashen waje.

Sai dai kuma a wannan karon, Manhaja ta tattaro cewa wani ma’aikacin hukumar, mai suna Polycarp, ya cika wandonsa da iska bayan ya haɗa bada bayanai kan kuɗin har Dalar Amurka 30,000.

Wasu daga cikin waɗanda su ka nemi a sakaya sunansu sun shaida wa wannan jarida cewa, daraktan shiyyar, Benedict Ubi, makonni biyu da suka gabata, ya ba da umarnin a binciki ɗakin ajiye kayan laifi sakamakon rikicin cikin gida da ya faru a Legas.

A cewar majiyoyin, lokacin da Polycarp ya samu umarnin cewa za a duba ɗakin sai ya ɗauki uzuri don ya samu hanyar guduwa.

“Nan da nan bayan an ba da odar tantancewa, sai ya ɗauki uzuri cewa zai je ya yi fitsari, daga nan kawai sai ya tsere. An yi ƙoƙarin jin ta bakinsa amma duk layukan wayarsa a kashe, inji majiyar.