Za mu kai hakimin Bichi fadarsa cikin lumana – Sarki Sanusi

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Mai Martaba Sarkin Kano, Muhammad Sanusi II, ya tabbatar wa mazauna yankin ƙaramar Hukumar Bichi da ke jihar Kano cewa, Masarautar za ta tabbatar da an kai musu Hakimin su, Munir Sanusi Bayero, domin ya ci gaba da gudanar da aikinsa cikin lumana a Bichi.

An bayyana cewa jami’an ‘yan sanda da jami’an DSS sun tare hanyar shiga fadar Gidan Rumfa, inda suka hana zirga-zirgar shiga da fita.

Ko da yake ‘yan sanda da sauran hukumomin tsaro ba su bayyana dalilin ɗaukar matakin ba, amma majiyoyi sun ce ci gaban ya na da nasaba da naɗin sabon Hakimin Bichi, Munir Sanusi, wanda Sarkin ya ce za a yi masa rakiya a hukumance.

Wasu kuma sun ce wannan katangar na da nasaba da shirin tattaunawa da wasu masana tattalin arziki a kan ƙudirin sake fasalin harajin da ya janyo cece-kuce.

Tuni dai gwamnatin jihar Kano ta fusata kan lamarin, inda ta zargi gwamnatin tarayya da alhakin ɗaukar nauyin jami’an tsaro.

Sai dai Sarkin a ranar Larabar da ta gabata, yayin da yake karɓar tawagar Bichi da suka zo yi masa godiya bisa naɗin da aka yi masa tare da yi masa rijista, ya ce har yanzu ba a samu cikakken bayani kan dalilin da ya sa aka rufe fadar ba.

“Wannan abu da ya faru ya dagula hankali ne kawai, har yanzu ba mu san dalilin da ya sa hakan ya faru ba kuma waɗanda ke da hannu ba su faɗi dalilin da ya sa suka aikata hakan ba. Duk da haka, wannan ba zai hana komai ba.

“Ina mai tabbatar muku da cewa za a saka wata rana kuma za’a kawo muku Hakimin ku kuma komai zai gudana cikin kwanciyar hankali.”

Sai dai ya yi kira ga al’ummar Bichi da su kwantar da hankula su ci gaba da zaman lafiya kamar yadda aka san su.

“Je ka sanar da jama’a su ci gaba da zaman lafiya da addu’a. Koma dai halin da ake ciki, tabbas zaman lafiya da addu’a za su kai mu ƙarshen ramin.

“Duk lokacin da kuka ga mutum yana ƙoƙarin karya zaman lafiyar da jama’a ke jin daɗi, ba za ku shiga cikinsa ba,” in ji shi.

Ya kuma bayyana cewa Bichi ya kasance gida na biyu a gare shi tun yana girma kuma wurin da yakan shafe tsawon tsawon hutun da yake yi.

“Ban san inda ya wuce Bichi ba, watakila wasunku za su san da hakan idan sun samu damar yin mu’amala ko alaƙa da kawuna, Wambai Abubakar. Lokacin girma, duk lokacin da aka yi hutu mai tsawo a kowace shekara, nakan ziyarci Azare, inda na yi wata guda, sai Bichi inda na yi kwana ashirin da Dawakin Tofa na kwana goma. Haka na yi dogon hutuna tsawon lokacin da nake makaranta.

“A bayyane yake cewa duk garin da ka ziyarta don kwana ashirin a duk shekara, to haƙiƙa wani gida ne. Na san mutanen Bichi kuma na san su mutane ne masu son zaman lafiya. Haka nan kasa ce mai ilimi da kyakkyawar aƙidar addini.

“ƙari akan haka, da yadda mutanen Bichi suke girmama Halifa da Wambai Abubakar, babu yadda za a yi a kai musu dan Kalifa a matsayin Wambai su juya masa baya,” in ji Sarkin.

Shugabannin ’yan Bichi da ke fadar sun samu jagorancin Shugaban ƙaramar Hukumar Hamza Sule Maifata da Babban Limamin ƙaramar Hukumar, Malam Lawan Abubakar da Shugaban ƙungiyar Dattawa, Malam Isyaka Bichi.