Daga AMINA YUSUF ALI
Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya yi barazanar gurfanar da bankunan da suke cinikayyar Dala ba bisa ƙa’ida ba. Wato ta haramtacciyar hanya. Sannan kuma a gurfanar da wannan banki da ya karya doka a gaban kuliya.
Gwamnna riƙon ƙarya na CBN, Folashodun Shonubi, shi ya bayyana haka a wata lacca da aka gabatar a kan samar da mafita ga tattalin arzikin Nijeriya, wanda aka yi a Abuja. Taron ya mai da hankali a kan yadda za a katange shigar da kuɗaɗen gwamnati zuwa haramtacciyar hanya tare da shigar da su inda ya dace don kawo cigaban tattalin arzikin gwamnati.
Shonubi ya ba da sanarwar cewa, zai haɗa kwamitin da zai fara kai ziyarar ba-zata zuwa bankunan da ake zargi da sayar da Dala ba bisa ƙa’ida ba. Sannan duk banki da aka tabbatar yana wannan harƙalla, za a gurfanar da shi a gaban hukuma saboda ladabtarwa.
“Akwai bukatar mu zayyano sunayen bankunan kasuwancin da suke aikata wannan ta’a ‘sa kuma mu kunyata su”.
Hakazalika, wannan gwamna na riƙon ƙwarya ya bayyana matsaloli da naƙasu da suke tattare da tsarin yadda kuɗaɗen suke shiga aljihun gwamnati a halin yanzu. Don haka a cewar sa, da sake, duba da irin maqudan kuɗaɗen da suke kewayawa a halattattun cibiyoyin yin halastaccen cinikin kuɗi.
A cewar sa, saboda son mutane su dinga cinikin canjin ta halastacciyar hanya ya sa aka yi musu ragin Naira 5 a kan halastaccen canji yayin da mutane suka guje mata kuma ya sa ita ma gwamnati ta janye wannan ragi na Naira 5.
Daga ƙarshe dai Gwannan CBN ya bayyana alfanu da fa’idoji na kiran mutane zuwa halastacciyar cinikayyar Dala. Sannan ya bayyana cewa, za a sake wa kasuwar canji suna daga I & E market, zuwa Kasuwar Canjin kuɗin ƙasar waje ta Nijeriya. Domin ita kaɗai ce kafar canjin suka yarda da ita.