Ma’aikatun ministoci:Yadda Tinubu ya shammaci ’yan Nijeriya

*Malagi da sauran ministoci za su sha rantsuwa ranar Litinin
*A karon farko Kano ba ta da babban minista
*Ɗan Kudu ya zama Ministan Abuja bayan shekaru masu yawa
*Tsohon gwamna ya zama ƙaramin minista
*Wataƙila Gawuna ya samu kujerar babban minista daga Kano

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

A ranar Laraba, 16 ga Agusta, 2023, Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya shammaci masu lura da al’amuran yau da kullum da sauran al’ummar ƙasar bayan da ya sanar da ma’aikatun da sababbin ministocinsa za su jagoranta.

Shugaba Tinubu zai rantsar da sabbin ministocinsa a ranar Litinin, 21 ga Agusta, 2023. Ministocin da za a rantsar sun haɗa da Shugaba kuma Mawallafin jaridun Blueprint da Manhaja, Alhaji Mohammed Idris Malagi, wanda zai jagoranci Ma’aikatar Yaɗa Labarai.

Za a rantsar da ministocin ne a ɗakin taro na Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja da misalin ƙarfe 10 na safe.

Wani babban abin da Tinubu ya yi shi ne naɗa tsohon Gwamnan Jihar Ribas, Nyesom Wike, a matsayin ministan babban birnin tarayya Abuja, wanda hakan ya savawa ƙa’idar ‘yan Arewa waxanda galibi ke riƙe da muƙaman a baya.

Baya ga Mobolaji Ajose-Adeogun (1979-82) da Emeka Okoye (1981-84), duk ministocin da suka biyo baya sun fito ne daga Arewa.

Wata sanarwa da Daraktan Ofishin Yaɗa Labarai na Sakataren Gwamnatin Tarayya, Willie Bassey, ya fitar a ranar Laraba ta ce, an bai wa ministocin damar zuwa da baƙi biyu kowanne.

“Masu girma ministocin da za a rantsar ana sa ran za su zo da baqi biyu kowanne. Dukkan ministoci da baƙi za su zauna da ƙarfe 9:00 na safe.”

Wani abin mamaki a naɗe-naɗen rabon ma’aikatun shine, yadda aka naɗa tsohon Gwamnan Jihar Zamfara, Muhammad Bello Matawalle, a matsayin Ƙaramin Minista, inda hakan ya saɓa da al’adar gwamnatocin Nijeriya, waɗanda su kan fifita tsofaffin gwamnoni wajen naɗin muqamin minista, inda ake ba su babban minista maimakon ƙarami.

A ranar Laraba Fadar Shugaban Ƙasar ta sanar da ma’aikatun da sabobbin ministocin za su riƙe.

Bugu da ƙari, wani abin al’ajabi shine, yadda aka naɗa babba da ƙaramin ministan tsaro daga yanki guda, wato tsohon Gwamnan Jihar Jigawa, Mohammed Badaru Abubakar a matsayin Ministarn Tsaro, yayin da Matawalle zai kasance ƙaramin ministan ma’aikatar, waɗanda dukkansu daga Arewa maso yamma suka fito.

Tinubu ya fara miqa sunan mutum 28 ne ga majalisa don tantance su, a ranar 27 ga watan Yuli, sannan ya ƙara tura mata ƙarin sunayen a cikin watan Agusta.

Majalisar Dattawan Nijeriyan ta amince da 45 daga cikin mutum 48 da Shugaba Tinubu ya aike mata yayin da ta ƙi tabbatar da uku a ciki, da suka haɗa da tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai da Stella Okotete daga jihar Delta da kuma Ɗanladi Abubakar daga jihar Taraba.

Haka nan wani abin mamaki shine, yadda duk da girman Jihar Kano da yawan jama’arta da kuma muhimmancinta a siyasar Nijeriya, wannan shine karo na farko da ba ta da babban minista. An naɗa mata tsohon Mataimakin Gwamnan Jihar Abudullahi Tijjani Gwarzo a matsayin Ƙaramin Ministan Ayyuka da Mariya Mahmud a matsayin Ƙaramar Ministar Babban Birnin Tarayya Abuja. A bisa la’akari da tarihi, a na bai wa Kano manyan ministoci guda biyu ne.

To, sai dai kuma wata majiya ta shaida wa Blueprint Manhaja cewa, wataƙila an ajiye kujerar babban minista ne ga ɗan takarar Gwamnan Jihar Kano na Jam’iyyar APC a zaɓen da ya gabata, Nasiru Yusuf Gawuna, ne, idan har bai samu nasara a kotun zaɓe da ya ke ƙalubalantar gwamna mai ci, Abba Kabir Yusuf na Jam’iyyar NNPP.

A cikin takardar sanarwar bikin rantsar da ministocin, an lissofo sunayensu da ma’aikatar da aka tura kowanne kamar haka:  

Ministan Sadarwa da Tattalin Arziki na Zamani – Bosun Tijani; Ƙaramin Ministan Muhalli – Ishak Salaco; Ministan Kuɗi da Tattalin Arziki – Wale Edun; Ministar Harkokin Teku da Tattalin Arziki – Bunmi Tunji; Ministan Lantarki – Adedayo Adelabu; Ƙaramin Ministan Lafiya da Walwalar Al’umma – Tunji Alausa;  Ministan Ma’adanai – Dele Alake;  Ministan Yawon Buɗe-Ido – Lola Ade-John;  Ministan Sufuri – Adegboyega Oyetola;  Ministan Kasuwanci da Zuba Jari – Doris Anite;  Ministan Wasanni – John Enoh;  Ministan Abuja – Nyesom Wike;  Ministar Al’adu – Hannatu Musawa; Ministan Tsaro – Muhammad Badaru;  Ƙaramin Ministan Tsaro – Bello Matawalle; Ƙaramin Ministan Ilimi – Yusuf T. Sununu;  Ministan Gidaje da Bunƙasa Birane – Ahmed M. Dangiwa; Ƙaramin Ministan Gidaje da Bunqasa Birane – Abdullah T. Gwarzo; Ministan Kasafi da Tsare-Tsare – Atiku Bagudu; Ministan Muhalli (Kaduna); Ƙaramar Ministar Abuja – Mairiga Mahmud; Ministan Albarkatun Ruwa – Bello M. Goronyo.

Sauran sun haɗa da: Ministan Noma da Samar da Abinci – Abubakar Kyari; Ministan Ilimi – Tahir Maman; Ministan Harkokin Cikin Gida – Sa’Idu A. Alkali; Ministan Harkokin Waje – Yusuf M. Tuggar; Ministan Lafiya da Walwalar Jama’a – Ali Pate; Ministan Harkokin ‘Yan Sanda – Ibrahim Geidam; Ƙaramin Ministan Ƙarafa – U. Maigari Ahmadu; Ministan Ƙarafa – Shuaibu A. Audu; Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai – Muhammed Idris; Ministan Shari’a – Lateef Fagbemi; Ministan Ƙwadago da Samar da Ayyuka – Simon B. Lalong.

Ragowar su ne: Ƙaramar Ministar Harkokin Cikin Gida – Imaan Sulaiman-Ibrahim; Ministan Ayyuka na Musamman – Zephaniah Jisalo; Ministan Albarkatun Ruwa – Joseph Utsev; Ƙaramin Ministan Noma da Samar da Abinci – Aliyu Sabi Abdullahi; Ministan Kimiyya da Fasaha – Uche Nnaji; Ƙaramar Ministar Ƙwadago da Samar da Ayyuka – Nkiruka Onyejeocha; Ministar Harkokin Mata – Uju Kennedy; Ministan Ayyuka – David Umahi; Ministan Sufurin Jiragen Sama – Festus Keyamo; Ministan Matasa – Abubakar Momoh; Ministar Agajin Gaggawa da Rage Talauci – Betta Edu; Ƙaramin Ministan Albarkatun Iskar Gas -Ekperikpe Ekpo sai Ƙaramin Ministan Man Fetur – Heineken Lokpobiri.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *