Gwamna Dauda Lawal na Jihar Zamfara, ya jaddada cewa gwamnatinsa za ta bai wa fannin ilimin jihar muhimmaci ta hanyar ware masa kaso mai tsoka daga kasafin jihar na shekara-shekara.
Ya bayyana haka ne a lokacin da yake jawabi a wajen taron bikin maraba da sabbin ɗalibai wanda kwalejin Zamfara College of Arts and Science (ZACAS) da ke Gusau ta shirya a ranar Larabar da ta gabata.
Mai magana da yawun Gwamnan Jihar, Sulaiman Bala Idris, ya ce taron ya gudana ne a harabar Kwalejin da ke Gusau, babban birnin jihar.
Ya ƙara da cewa, Zamfara College of Arts and Science (ZACAS) na ɗauke da sassa daban-daban da suka haɗa sashen kimiyya da fasaha, sashen nazarin aikin jarida da dai sauransu.
Kazalika, ya ce an shirya bikin ne ga sabbin ɗalibai 2,369 da suka samu gurbin karatu a kwalejin na zangon karatun shekarar 2023/2024.
Ya ci gaba da cewa, Gwamna Dauda Lawal ya yaba da adadin ɗaliban da kwalejin ta yaye a shekarun baya, inda a cewarsa hakan ya ƙara bayyana irin ƙwazon da makarantar ke da shi.
“Gwamnan ya sha alwashin bai wa ‘yan jihar Zamfara ilimi mai nagarta ba tare da la’akari da bambancin matsayi ba don cigaban jihar,” in ji Idris.
A cewar Idris, tun farko sa’ilin da yake jawabi, “Shugaban Zamfara College of Arts and Science (ZACAS), Dr. Yakubu Sani, ya yaba wa Gwamna Dauda Lawal na zama kan gaba wajen bada tallafin karatu ga ɗaliban jihar.
“Ya ce sama da shekaru goma da suka gabata, duk shekara Gwamnan na ba da tallafin karatu ga ɗaliban ZACAD sama 200 daga aljihunsa.”