Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
A ranar Litinin ne ɗan takarar Shugaban Ƙasa na Jam’iyyar PDP kuma tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar ya yi iƙirarin cewa Shugaba Bola Tinubu na shirin ƙaddamar da tsarin farfaganda a cikin kwanaki masu zuwa.
Ya yi nuni da cewa, Tinubu ya riga ya naɗa mataimakansa a kafafen yaɗa labarai sama da 15 da nufin tura munanan bayanai a matsayin tsarin mulkin ƙasa da kuma kawar da hankalin ‘yan Nijeriya daga matsanancin zafin da gwamnatinsa ta jawo musu.
Mataimaki na musamman kan harkokin yaɗa labarai na Atiku, Phrank Shaibu, a cikin wata sanarwa, ya ce labarin ƙarya ne game da ɗage haramcin biza da Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa ta yi.
Ya lura cewa wannan shi ne salon Tinubu tun zamaninsa na gwamna kuma jagoran jam’iyyar sa.
Atiku ya ce: “Daga bayanan da muka samu, Bola Tinubu na shirin yin farfaganda don wuce gona da iri yayin da yake shirin halartar taron Majalisar Ɗinkin Duniya.
“Zai yi iƙirarin jawo hannun jarin waje da ya kai dala biliyan 100 amma ba zai ba da cikakkun bayanai ba. Duk farfaganda ce.
“A ƙasar Indiya, ya yi iƙirarin cewa sun karɓi alƙawuran sama da dala biliyan 14 kamar yadda magabacin sa, Shugaba Muhammadu Buhari, ya yi iƙirarin cewa a shekarar 2018 ya yi alƙawarin da ya kai dala biliyan 6. Wannan ba komai ba ne illa saka hannun jari a baki.
“Bayan tafiyarsa zuwa Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa, Tinubu ya yi iƙirarin cewa an ɗage haramcin biza nan take. Yanzu, sun canza sheƙa bayan hukumomin UAE sun bayyana cewa labarin ƙarya ne. Irin wannan abin kunya ne Nijeriya za ta ci gaba da jawowa a wannan kakar ta balablu.
“Bayan ya kasa kawo sake haifuwar tattalin arziki, yanzu ya ɗauki mataimakan yaxa labarai sama da 15 a maimakon ɗaukar ƙarin ƙwararan matakan farfaɗo da tattalin arziki.”
Jerin masu taimaka masa kan harkokin yaɗa labarai sun haɗa da: Ajuri Ngelale (Mai ba da shawara na musamman kan harkokin yaɗa labarai da yada labarai); Tunde Rahman (SSAP Media); Tope Ajayi (SSAP Media and Publicity); Abdulaziz Abdulaziz (SSAP Print Media) da sauran wasu mutum 10 dake taimakamasa a fannoni daban-daban.
Wannan baya ga ministan yaɗa labarai da wasu da aka naɗa a ma’aikatar domin tafiyar da ajandar farfaganda.
Shaibu ya ce abin dariya ne a ce Tinubu, wanda ya yi ƙasa a gwiwa tun daga ranar farko, ya gudanar da taron majalisar ministocin sau ɗaya kacal tun bayan rantsar da shi kusan kwanaki 120 da suka gabata.
Ya roƙi ‘yan Nijeriya da su ci gaba da haƙuri yayin da Kotun Ƙoli ke shirin fara aiki kan ɗaukaka ƙarar zaɓen.
“Tinubu ya cire tallafin mai ba tare da wani shiri ba kuma ya yanke shawarar miƙa ‘yan buhunan shinkafa ga miliyoyin talakawan Nijeriya. Har zuwa yau, mafi ƙarancin albashi ya rage Naira 30,000 ko dala 31 a kowane wata bisa la’akari da farashin canji na kasuwa.
“Wannan shi ne hukuncin da ‘yan Nijeriya ke fuskanta domin Hukumar Zaɓe ta kasa yin aikinta a ranar 25 ga watan Fabrairu. Wannan wata alama ce ta kalaman littafi mai tsarki, wanda ya ce idan adalai suka jagoranci jama’a suna murna, amma lokacin da miyagu ke mulki, mutane suna shan wahala.
“A halin yanzu, muna roƙon ‘yan Nijeriya da su yi haƙuri yayin da hukumomin shari’a ke gudanar da aikinsu na gyara maguɗin zaɓe da ya durƙusar da ‘yan Nijeriya.”
