SERAP ta maka Tinubu a kotu kan tsoffin gwamnonin da ya naɗa ministoci suke karvar fansho

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Ƙungiyar Kare Haƙƙin ‘Yan Ƙasa da Tabbatar da Shugabanci Nagari a Nijeriya (SERAP), ta kai ƙarar Shugaba Bola Tinubu kotu kan gazawarsa wajen hana tsofaffin gwamnonin da suke riƙe da muqamin minista karɓar kuɗaɗen fansho na jihohi.

Ƙungiyar SERAP dai na neman kotu ta tilasta wa Tinubu ya umarci waɗannan tsofaffin gwamnonin da su daina karvar irin waɗannan kuɗaɗe.

A wata sanarwa da ƙungiyar ta fitar a ranar Lahadi, mataimakin shugaban ƙungiyar a Nijeriya, Kolawole Oluwadare, ya ce ministocin da abin ya shafa su ne Nyesom Wike da Bello Matawalle da Adegboyega Oyetola.

Sauran tsofaffin gwamnonin sun haɗa da Badaru Abubakar da David Umahi da Simon Lalong da Atiku Bagudu da kuma Ibrahim Geidam.

Sanarwar ta ce “Naɗin waɗanda ke karɓar fansho na rayuwa a matsayin ministoci wani aiki ne na son rai da kuma saɓa wa ƙa’ida.”

“Yayin da da yawa daga cikin ‘yan waɗanda suka ajiye aiki ba a biyan su kuɗaɗen fansho ba, tsofaffin gwamnonin da ke riqe da muƙamin minista na samun maƙudan kuɗaɗen alawus-alawus idan sun bar ofis.

“Gwamnatin Tinubu tana da ƙarfin hana tsofaffin gwamnonin karɓar duk wani haƙƙi na ritaya yayin da suke aiki a matsayin ministoci.”

SERAP dai ta ce wannan ɗabi’a ba ta dace ba, musamman idan aka yi la’akari da ƙalubalen tattalin arzikin da ƙasar ke fuskanta.

Sai dai kuma har yanzu ba a sanya ranar fara sauraron ƙarar ba.

By Editor