Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano
Sabon Kwamishinan Ma’aikatar Ruwa na Jihar Kano Hon. Umar Haruna Doguwa ya ce a za su yi duk abinda ya kamata don ganin gwamnatin Kano ta sauke alƙawarin da ta ɗauka akan kyautata cigaban al’ummar Kano.
Ya bayyana haka ne a lokacin da tawagar al’ummar masu ruwa da tsaki daga ƙaramar hukumar Doguwa suka yi masa rakiya ya karɓi aiki daga tsohon kwamishinan ma’aikatar ruwa da aka mayar ma’aikatar ilimi Gwani Ali Haruna Makoɗa a ma’aikatar ruwa ranar Talata.
Ya ce daga abinda yake alfahari da shi a matsayin da ya yi na kwamishinan ilimi shine yadda ya yi aiki tuƙuru mutane daga gida da sassan duniya suka amince Gwamna Abba Kabir Yusuf ya ɗauki layin gyaran ilimi suke ta bashi lambobin yabo akan ilimi, haka yake so su yi irin wannan aiki a ma’aikatar ruwa da ya dawo don ganin an ɗora Kano akan samun ruwan sha.
Hon. Haruna Doguwa ya ce yana jin daɗi da a cikin ‘yan shekarunsa ya yi Kwamishina a ma’aikatu uku a jihar Kano ba don ya fi kowa ba, Allah ne ya so ya yi masa hakan, yana kuma godiya ga Allah da wannan dama da ya ke ba shi.
Ya yaba da irin ƙoƙari da Kwamishina da ya canza Gwani Ali Haruna Makoɗa ya yi na samar da ruwan sha ga al’ummar Kano sannan ya yi kira ga mutanen Kano su ƙara haƙuri gwamnati na aiki domin kawo ƙarshen matsalar wahalar ruwa, inda ya ce akwai injuna da aka yi oda za su zo da za a yi amfani da su wajen samar da ruwa da sauran ayyuka da ake ta yi na samar da ruwa a jihar Kano.
Hon. Doguwa ya ce mai girma Gwamnan Jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf da gaske yake kuma cikin yardar Allah za su yi aiki tuƙuru wajen samar da ruwa a Kano.
Shi ma da yake zantawa da ‘yan jarida bayan tarbar sabon Kwamishinan na ma’aikatar ruwa. Babban sakatare na ma’aikatar, Injiniya Abdulrazak Haruna, ya bayyana cewa Gwani Ali Haruna Makoɗa tsohon Kwamishinan ma’aikatar shugaba ne nagari mai dattako duk da bai daɗe da zama da shi ba, amma ya same shi mai ƙudiri mai kyau ga al’ummar Kano da ya bada kyakkyawan gudunmuwar yin aiki a ma’aikatar ruwa suna fata inda ya koma ma’aikatar ilimi ya ɗora yadda ilimi zai cigaba da haɓaka.
Babban sakataren na ma’aikatar ruwan na jihar Kano ya ce suna yi wa sabon Kwamishinan da aka kawo Hon. Haruna Doguwa albishir da cewa zai samu ma’aikata masu aiki tuƙuru da ƙwazo da bashi cikakken haɗin kai da goyon baya domin kaiwa ga nasara kamar yadda aka baiwa tsohon Kwamishina.
Babban Sakataren na ma’aikatar ruwa, Injiniya Abdulrazak Haruna ya ce Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf mutum ne mai son cigaban jihar Kano domin duk abinda ya shafi ma’aikatar ruwa idan aka kai masa nan da nan yake bada amincewa aje a gudanar suna fata Allah ya cigaba da riƙo da hannunsa da dukkan masu aiki da shi.
Shugaban Jam’iyyar NNPP na ƙaramar hukumar Doguwa, Alhaji Auwalu Doguwa da yake cikin tawagar da suka rako Kwamishinan Haruna Doguwar ya gode wa Gwamna Abba Kabir bisa aiki da yake da Haruna Doguwa suna kuma alfahari da irin muƙamai da yake yi yi na Kwamishina a ma’aikatu uku tun daga na ilimi mai zurfi ya dawo ya yi na ilimi yanzu aka dawo da shi na ruwa suna alfahari da abinda ya yi na jagorantar kai ɗalibai ƙasashen duniya lokacin Kwankwaso kuma ya dawo a wannan gwamnati ya bada gudunmuwa wajen gyara ilimi suna fata zai yi aiki tuƙuru a ma’aikatar ruwa da aka dawo da shi don ya wadata jihar Kano da ruwa.
