Zafin kishi ya sa uwa kashe ’ya’yanta biyar

Wata kotu ta yanke wa wata mata a birnin Solingen na yammacin ƙasar Jamus hukuncin ɗaurin shekaru 15 bayan samunta da laifin kashe biyar daga cikin ’ya’yanta na cikinta guda shida.

Yaran da ta halaka ƙanana ne, domin bas u ma wuce shekara ɗaya zuwa takwas ba.

Kotun wacce ke da zama a birnin Wuppertal ta ƙasa gano wani dalili da zai sa a yi wa matar mai shekaru 28 a duniya uzuri, saboda haka ta soke batun sakinta bayan kammala wa’adin shekaru 15 a gidan yari.

A yayin shari’ar, mai shigar da ƙarar ya yi zargin cewa ta fara ɗauke wa yaran hankali ne sannan ta fara jefa su ruwa ko ta shaƙe su ɗaya bayan ɗaya ba bu tausayi ba bu jin ko a jikinta.

Jami’an da ke binciken lamarin sun yarda cewa ganin hoton mijinta da sabuwar matarsa shine ya tunzura matar aikata ta’asar, wanda ya gigita ƙasar Jamus.

Bayan nan ta aika masa da saƙon cewa ba zai sake ganin ’ya’yan ba. An gano gawarwakin yaran a gadajensu a ranar 3 ga watan Disamban 2020.

Matar ta dage cewa wani ne ya shigo gidanta, ya ɗaure ta sannan ya tursasa ta aika saƙon kafin ya kashe yaran. Ƙwararrun likitocin mahaukata ba su sami wata shaida ta mummunar taɓin hankali tare da ita ba.

Lauyan da ke kare ta ya nemi a sake ta bisa hujjar cewa akwai kokwanto kan ko wacce yake karewa ce ta aikata kisan. Kotun ta gano cewa mahaifiyar yaran wacce ta sha jefa kanta a gaban jirgin qasa da ke tafiya a tashar Dusseldorf ce ta kashe su.

Yaran sune; Melina, 1, Leonie, 2, Sophie, 3, Timo, 6, da Luca, 8. Ta tura babban ɗanta wanda ya tsira zuwa wajen kakarsa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *