Zamfara: AGILE ta wayar da kan al’ummar Bakura da Maradun kan sanya ‘ya’ya mata a makaranta

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau

Adolescent Girls Initiative for Learning and Empowerment (AGILE), wani shiri ne na bankin duniya tare da haɗin gwiwar ma’aikatar ilimi ta jihar Zamfara ta wayar da kan al’ummar ƙananan hukumomin Bakura da Maradun kan shirin sanya ‘ya’ya mata a makarantu.

An gudanar da taron wayar da kan jama’a na kwana ɗaya a makarantar sakandiren gwamnati ta Agwaragi da ke garin Talatan Mafara hedikwatar ƙaramar hukumar Talata Mafara jiya Alhamis.

Da yake jawabi ga mahalarta taron mai kula da ƙananan hukumomin Bakura Maradun Alh. Mainasara Moyi Kaura ya bayyana cewa, maƙasudin gudanar da gangamin shi ne faɗakar da al’umma muhimmancin sanya ‘ya’yansu musamman mata a makaratar Boko domin su samu ilimin zamani.

A cewarsa, ɗaliban da za su ci gajiyar shirin sun ƙunshi ‘yan aji ɗaya daga JSS1 zuwa SS1.

Ya ce duk ɗalibin da ya yi rajista za a ba shi kyautar tsabar kuɗi Naira 60,000 a kowane zango a ƙarƙashin shirin AGILE na bankin duniya, inda ya ce an ba da muhimmanci ga yara mata masu ƙaramin ƙarfi musamman a ƙananan hukumomin jihar. 

Ya kuma ƙara da cewa tuni aka fara bayar da tallafin kuɗin shigar yara mata na JSS1 da ɗaliban SS1 N60,000 da aikin AGILE a ke gudarwa a halin yanzu a faɗin jihar.

Ya yi nuni da cewa a ƙarƙashin shirin za a ba kowace yarinya Uniform, kayan rubutu da sauran kayan koyo da koyarwa kyauta.

“Manufar ci gaban ayyukan AGILE shine inganta damar samun ilimin sakandare a tsakanin ‘yan mata,” ya ce.

Hakimin Gamji da ke ƙarƙashin masarautar Bakura, Alhaji Ibrahim Bello ya yabawa gwamnatin jihar Zamfara da bankin duniya bisa ɓullo da shirin AGILE na bunƙasa harkar ilimi a jihar.